Shugaban Amurka Joe Biden ya ce bai ga dalilin da zai sa Najeriya ta rasa kujerar dindindin a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ba.
Biden ya faɗi haka a lokacin tattaunawa ta wayar tarho da ya yi da shugaban Najeriya Bola Tinubu.
Shugaban Biden ya ce, Amurka na ƙoƙarin ganin cewar nahiyar Afirka ta samu kujeru 2 a kwamitin tsaro na Majalisar ɗinkin Duniya.
A cewar ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Tuggar lokacin da yake tabbatar da ganawar shugabannin biyu. ya ce “Shugaba Biden ya nanata cewar bai ga dalilin da zai sa Najeriya ba za ta samu ɗaya daga cikin kujerun kwamitin tsaro na Majalisar ɗinkin Duniya ba, duba da irin matsayin ƙasar a nahiyar Afirka da muhimmancinta.”
Tattaunawar shugabannin ta mayar da hankali kan alaƙa tsakanin ƙasashen biyu wurin tabbatar da bin doka da oda da kuma batun sakin shugaban kamfanin Binance da ke hada-hadar kuɗin internet Tigran Gambaryan.
A nashi ɓagaren shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gode wa shugaban Amurka kan haɗin gwiwa da aiki tare a fannonin tsaro a nahiyar Afirka da ma Afirka ta yamma.