Saudiyya za ta tallafa wa ‘yan gudun hijira a Najeriya, Chadi, da sauransu

Masarautar Saudiyya, ta hannun Cibiyar Bayar da Agajin Gaggawa ta Sarki Salman ta tara sama da dalar Amurka biliyan 1.1 da ƙudurin tallafa wa ‘yan gudun hijira a yankunan Sahel da tafkin Chadi.

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ofishin jakadancin Saudiyya a Najeriya ya fitar.

A cewar sanarwar, an yi alkawarin bayar da tallafin ne ta hanyar gudunmawar ƙasashe, hukumomi, da ƙungiyoyi masu bayar da agaji fiye da 10 da suka sadaukar da kansu don magance ƙaruwar buƙatun jin kai a waɗannan yankuna da ke fama da rikici.

An gudanar da taron masu ba da taimako tare da haɗin gwiwa da ƙungiyar haɗin kan ƙasashen Musulmi (OIC), da kuma ofishin Majalisar ɗinkin Duniya mai kula da harkokin jin kai (OCHA).

Taron ya kuma samu halartar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar ɗinkin Duniya a matsayin abokiyar huldar ta don ba da agajin gaggawa ga al’ummar Najeriya da Nijar da Chadi da Burkina Faso da kuma Mali, waɗanda suka fuskanci matsaloli da bala’o’i daban-daban.

A cikin jawabinsa yayin taron, mai ba da shawara a kotun masarautar kuma babban mai kula da agajin KS, Abdullah Al Rabeeah ya nuna jin daɗinsa ga wannan karamci da masu bayar da agaji suka nuna.

Ya ce, waɗannan gudunmawar ba wai kawai suna nuna haɗin kai ba ne, har ma suna bai wa ƙungiyoyin agaji damar ba da tallafin ceton rai.

Rabeeah ya ci gaba da cewa gudunmawar za ta tabbatar da tsaro da juriya ga al’ummar da abin ya shafa.