Ban janye daga takarar Gwamnan Jihar Kaduna ba – Sani Sha’aban

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ɗan takarar kujerar Gwamna a Jihar Kaduna a ƙarƙashin Jam’iyyar ADP, Honorabul Sani Sha’aban, ya bayyana cewa maganganun da wasu ke yi cewa ya janye takararsa bai san wannan zancen ba, domin kuwa shi ma ji ya yi kamar almara.

Ɗan takarar, wanda ya bayyana cewa duka ‘yan takarar da ke neman Gwamna a Jihar Kaduna ‘yan’uwa ne domin duk daga Zazzau suka fito, ya bayyana cewa shi bai ƙullaci kowa ba, kuma ba shi da niyyar ƙullatar wani a zuciyarsa.

Ɗan takarar, wanda ke magana a cikin wata hira da aka yi da shi ta musamman, ya bayyana maganganun janyewar tasa har sun ɓata ran cibiyar jam’iyyar ta ƙasa, inda ya ce, “Abin har ya vata wa uwar jam’iyyar rai har sun saki sanarwa a kan cewa ADP mai littafi babu inda ta je ta zauna ta ce ɗan takararta ya janye.”

Ya ma bayyana cewa suna ziyartar juna, ana zumunci tun da ‘yan siyasa suke, amma dai ba a yi yarjejeniya da shi ba.

Dangane da nasararsa, ya bayyana cewa tafiyarsa ta riga ta yi nisa, babu abin da zai ce wa Allah sai godiya, inda ya bayyana cewa Jam’iyyar LP ta yi ƙarfi a Kaduna, amma kashi 80 sun koma ADP.

Da yake magana dangane da salon yaƙin neman zaɓensa, Alhaji Sani Sha’aban ya bayyana cewa, tafiyar 2007 daban take da ta 2011, ita kuma daban take da shekarar 2015, domin a misalin da ya bayar, takarar Buhari akwai lokacin da ake da Boko Haram, akwai lokacin da in za ka tafi Abuja daga Zazzau za ka dinga ganin shingayen sojoji, sai ya ce a kamfe ɗinsa ba ya kwasar motoci masu yawa ya tafi, mutane ke bi wuri zuwa wuri da hotonsa su roƙi alfarma, yakan tara mutane na unguwa ne a sha shayi tare, ya gan su, su ganshi, ba a ganin tawagarsa domin kada ya sa mutane cikin haɗari.

Ɗan takarar ya bayyana cewa mutane na matuƙar son takararsa, ana tsayar da shi a gefen titi, a wurin taro, wurin jana’iza a nuna ana so ya fito, wasu ma sun bar jam’iyyun su sun dawo tafiyarsa, inda ya ce kashi 75 na mutanen Kaduna sun yi amanna sun karanta zuciyarsa sun yarda lallai akwai wani nono da zai tarfa a garinsu.

Ɗan takarar, wanda ya yi bayani dangane da irin wahalar da mutane ke fuskanta a ɓangaren ƙarin kuɗin makaranta da ilimi, ya bayyana cewa fastocinsa wasu ke yi, huluna da ƙananan riguna, da tallarsa al’umma ke yi, kuma Musulmi da Kiristoci.