Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja, Nyesom Wike, a ranar Talata ya ce bai yi nadamar juya wa jam’iyyar PDP baya ba a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Wike, wanda ya yi magana a gidan Talabijin na Channels a shirin siyasa A Yau, ya musanta cewa yana aikata ayyukan da bai dace ba ta hanyar ƙin goyon bayan Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a lokacin.
Ya kare matakin da ya ɗauka, inda ya ce an ɗauki matakin ne domin a yi adalci da gaskiya.
“A zaɓen shugaban ƙasa, na ce zan goyi bayan daidaito, gaskiya da adalci. A ɗaya ɓangaren kuma, zan goyi bayan jam’iyyata, shi ya sa muka ci zaɓen gwamna da zaɓen ’yan majalisar tarayya,” inji Wike.
“A ɓangaren zaɓen shugaban ƙasa, ban goyi bayan Atuliku ba ne saboda ban yarda da zalunci ba. A yau mutane suna cewa ‘a ladabtar da Wike, ya juya wa jam’iyyarsa baya.’ Ni ban yi adawa da jam’iyya ba,” in ji Wike.
A ƙoƙarin da ake na tunkarar babban zaɓe na 2023, Wike, gwamnan jihar Ribas, ya haɗa kai da wasu gwamnoni huɗu na jam’iyyar PDP, waɗanda suka haɗa da Samuel Ortom (Benuwai), Seyi Makinde (Oyo), Okezie Ikpeazu (Abia), da Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu), don daƙile Atiku.
Gwamnonin biyar dai sun tsaya tsayin daka wajen neman Sanata Iyorchia Ayu ya sauka daga muƙaminsa na shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa a matsayin wani sharaɗi na goyon bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar.
Daga baya Atiku ya sha kaye a zaɓen shugaban ƙasa a hannun ɗan takarar jam’iyyar APC na lokacin, Bola Tinubu, wanda a gwamnatinsa yake riƙe da muƙamin minista.
