Dalilin jihohi na karɓar rance duk da kasonsu na Asusun Tarayya

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Alƙaluma daga Ofishin Kula da Basussuka (DMO) sun nuna cewa a cikin watanni shida na farko bayan hawansu mulki, sabbin gwamnoni 13 sun karɓi bashin Naira biliyan 226.8 daga hannun masu kuɗi na cikin gida da waje.

A ci gaba da nazarin alƙaluman, an kuma nuna cewa ƙarin wasu gwamnoni 16 ne suka bayar da gudunmawa wajen ƙaruwar basussukan, ta hanyar ƙara adadin basussukan jihohinsu da Naira biliyan 509.3, wanda ya ƙunshi Naira biliyan 243.95 daga masu lamuni na cikin gida da kuma Dala miliyan 298.5 (N265.37) daga ƙasashen waje da hukumomi kamar Bankin Duniya da Asusun Ba da Lamuni na Duniya.

Taɓarɓarewar ta kuma nuna cewa jihar Kuros Riba ta samu lamuni yawa, inda ta samu Naira biliyan 16.2 daga cikin gida da dala miliyan 57.95 daga Aasashen waje. Jihar Katsina ta biyo baya da ƙaruwar basussukan daga Naira biliyan 62.37 zuwa Naira biliyan 99.3 a watan Disambar 2023, wanda ya kai Naira biliyan 36.93.

Jihar Neja ta zo ta uku, inda ta samu ƙari daga Naira biliyan 121.95 zuwa Naira biliyan 139.8 na bashin cikin gida a daidai wannan lokacin, wanda ya kai Naira biliyan 17.85. Filato, Ribas, Zamfara, da Abuja suma sun tsunduma cikin ayyukan lamuni a cikin gida.

A ɓangaren basussukan ƙasashen waje, jihar Ebonyi ta tara dala miliyan 37.54, yayin da jihar Kaduna ta ciyo bashin dala miliyan 17.69 daga hannun masu kuɗi daga waje. Hakazalika gwamnonin wasu jihohi kamar Kano, Neja, Filato da Sakkwato, Taraba, da Zamfara suma sun samu lamuni daga waje.

By ukarofi