Daga AISHA ASAS
Shahararren mai ɗaukar hoton nan da sunansa ya yi tambari a ƙwarewa ta vangaren samar da ingantattun hotuna, Malam Sani Mohammed Maikatanga, ya bayyana yadda ya ji yayin da ya samu tabbacin lashe gasar ɗaukar hoto ta Wiki Loves Africa, wanda ya bayyana cewa ba zato ba tsammani ya ji kansa a matsayin zakaran gasar. Ya kuma bayyana farin cikinsa kan cin gasar, wadda ke ɗauke da la’ada ta dalar Amurka 2,000.
A satin da ya gabata ne Manhaja ta ruwaito cewa, gasar wadda ta ginu akan sauyin yanayin duniya, abinda bature ke kira da ‘Climate & Weather’, mutum 13,413 daga ƙasashen Afirka 51 ne suka shiga gasar.
Maikatanga ya yi wa takwarorinsa zarra a gasar ne ta dalilin wani hoto da ya ɗauka mai alaƙa da sauyin yanayi a ƙauyen Auyo, Jihar Jigawa.
Ɗaya daga cikin alƙalan gasar, Juror Michale Maggas ya ce, “Hoton ya nuna haƙiƙanin al’amari a ƙauyukan da ambaliya ta shafa, yanayin launi da kuma kaifin sun sanya hoton zama mai ɗaukar hankali.”
Alƙalai waɗanda suka haɗa da ɗimbin ‘yan sa-kai, da kwamitin alƙalai gwanayen hoto na mutum 11 daga sassa daban-daban na duniya, sun yi nazarin kowane hoto, sauti da bidiyo da aka shigar, sannan daga ƙarshe, alƙalan na ƙasa da ƙasa suka zaɓi zakaru uku na gasar, kuma Maikatanga ne na farko a ukun.
Sauran kuwa sun haɗa da Mohamed Nasr daga Ƙasar Somaliya, da hotonsa na hadari da ya fuskanto wani sansanin ‘yan gudun hijira, sai na ukun su, Mohammed Osman daga Sudan, da hotonsa na wasu yara da ke tsaye a bakin gulbi.
A zantawarsa da Mujallar Fim, Maikatanga ya bayyana jin daɗin sa kan wannan nasara da ya samu, inda yake cewa, “abu ne da ban tava tunani ba. Saboda na san an ce Afrika, amma kuma sai Allah ya yi ikon sa kamar yadda na samu na lashe gasar ‘Global Landscape Forum Africa’ da aka yi a shekarar 2022, sai ga shi wannan ta ‘Wiki Loves Africa Photo Competition 2023’ ɗin da aka yi a kan ‘Climate & Weather’, ita ma na zama zakara.
Ina yi wa Allah godiya. Kuma ina gode wa alƙalan wannan gasar da su ka zavi hotona ya zama na ɗaya a cikin hotu sama da dubu goma sha uku da aka shiga da su gasar daga ƙasashe 51 na Afrika, amma ni daga Nijeriya kuma Jihar Kano na zama na ɗaya. Ina yi wa Allah godiya, kuma na yi farin ciki matuƙa.”
Wannnan nasara ba ta zama irinta ta farko da fasihin mai ɗaukar hoton ya samu ba, domin ko a shekarar 2022, Maikatanga ya lashe gasar ‘Global Landscape Forum Africa’.
