Karyewar gada a babbar hanyar Inugu zuwa Fatakwal a jihar Inugu, ta jefa al’ummar yankin cikin halin tsaiko.
Karyewar gadar a ranar Litinin da ta gabata, ta haifar da tsaikon zirga-zirga ga masu amfani da hanyar.
Bayanin haka ya fito ne daga bakin mai magana da yawun Gwamnan Jihar Inugu, Dan Nwomeh, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X (Twitter).
A cewar Nwomeh, gwamnati ta gargaɗi masu abubuwan hawa da su guji bin hanyar da ke tsakanin New Artisan da Naira Triangle a Jihar Inugu.
Ya ƙara da cewa, jami’an gwamnatin tarayya da jihar sun hallara wurin don ɗaukar matakin da ya dace.

Sai dai jami’in bai bayyana ko an samu asarar rai sakamakon iftila’in ba.