Daga MUHAMMADU MIJITTABA a Kano
Kasancewar tashar manyan motocin safa na Kano an samar da ita ne domin haɗa motocin safa-safa masu zirga-zirga tsakanin Kudanci da arewacin ƙasar nan da sauran sassan Nijeriya, wanda kuma an samar da wannan tashar ne a daidai lokacin da matsalar satar yara daga arewa zuwa Kudu, ko shigo da abubuwa masara kyau kamar miyagun ƙwayoyi da tabar wiwi, da sauran matsaloli da a wancan lokacin waɗannan motoci su kai ƙaurin suna aka samar da wannan tasha ta Luɗurious a Kano domin kawar da waɗannan matsaloli, wanda kuma a yanzu sai mu ce kwalliya ta biya kuɗin sabulu, domin kuwa wannan tasha an samu nasarar kashi 95 cikin 100 na kawar da matsalolin da aka koka akan irin waɗannan motoci bayan haɗa waɗannan motoci waje ɗaya da gwamnantin Kano ta yi a shekaru da suka gabata, kamar dai yadda shugaban tashar motocin safa-safa ta Jihar Kano, Alhaji Kabiru Yunusa, mai unguwar Kureƙen Sani ya bayyana a wata hira da ya yi da manema labarai da makon da ya gabata a Kano.
Haka kuma ya ƙara da cewa daga cikin nasarorin da suka samu sun daƙile satar yara daga Arewa zuwa Kudu aƙalla yara 16 da taimakon jami’an tsaro masu nagarta waɗanda ba bara gurbi ba, “domin komai akwai zakka a cikinsa za ka samu nagari da akasin haka, sai kuma samun nasara na daƙile fataucin mutune, shi ma da taimakon Allah da taimakon jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.
“Haka kuma akwai nasara wajen ƙoƙari da muke yi na hana shigowa da dukkan wani abu da doka ba ta yarda ba a wannan tasha ta safa-safa ta Kano, domin kuwa muna aiki da dukkanin hukumomin ‘yan sanda, Sibil Difense, KARoTA, Hisbah da sauransu wajen tsarkake wannan tasha daga duk wani abu na ba daidai ba a wannan tasha ta Luɗurious da ke Kano.”
Mai Unguwa Kurƙen Sani, ya ƙara da cewa, “wani abun takaici shi ne akwai lokacin da aka yi ƙoƙarin shigo da wata tabar wiwi, har da rakiyar wasu bara gurbin jami’an tsaro, amma haka ba ta bamu tsoro ba muka tunkaresu da haɗin gwiwar jami’an tsaro nagari, Allah ya ba da sa’a aka daƙile wannan mummunar niyya ta su ta shigo da abun da doka ba ta yarda da shi ba a Kano, don haka tashar dogayen motocin safa-safa da aka samar ta na taka muhimmiyar rawa wajen cimma burin da aka samar domin shi.”
Mai Unguwar Kureƙen Sani, shugaban tashar safa-safa na Kano ya bayyana takaicinsa a kan samu yadda ƙasa za ta yi aikinta daidai na daƙile ɓarna, amma sama ta warware, wanda kuma muke roƙon shugabanni da sauran masu ruwa da tsaki da a sanya tsoron Allah, kishin ƙasa tausayin al’umma da riƙe amanarsu domin bayan rayuwar duniya akwai wata rayuwar wanda kowannen mu yana son ya samu kyakkyawar makoma a ranar gobe.
A ƙarshe ya koka kan yadda matsalar duhu ke damun tashar safa-safa ta Kano da ma sauran tashoshin mota wanda muke roƙo ga Gwamnan Kano mai jin kukan jama’a a kowane lamari da ya kawo mana ɗauki a wannan tasha da ma sauran tashoshi baki ɗaya ta hanyar sanya fitilu masu aiki da hasken rana kamar yadda aka gwangwaje gwamnatin jihar Kano a kowane titi, inda kuma ya yaba wa Gwamnan Kano kan haɗin kai da ya ke bai wa wannan tasha dama sauran tashoshi dama ciyar da Kano gaba.
