Daga MUHAMMADU MIJITTABA a Kano
Shugaban riƙo na ƙungiyar kasuwar katako da ke Rijiyar Lemu a Jihar Kano, ya koka kan yadda akan rashin wuri ko kwandunan zuba shara ke barazana ga lafiyar ‘yan kasuwar da sauran maƙotansu, wanda kuma ya nemi agajin gaggawa daga Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf kan kawo masu agajin gaggawa na samar da wuraren zuba shara wanda babu wani abu da yafi ƙarfin gwamnati ta yi wa al’umma musamman ganin yadda wannan gwamnati ta Kano ta zage damtse wajen ganin komai ya tafi daidai a jihar, kamar dai yadda shugaban riƙo na ƙungiyar kasuwar katakon Alhaji Yusuf Tanko Abdullahi ya bayyana a yayin wata ganawa da manema labarai kan matsalar shara da ta addabi kasuwar.
Haka kuma Alhaji Yusuf Tanko Abdullahi ya ƙara da cewa su a ƙungiyance sun yi iya ƙoƙarin su na tsaftace kasuwar a zahiri da kuma baɗini domin kuwa a da can mota ba ta shiga kasuwa ta ko’ina amma yanzu gashi ko’ina mota na shiga kuma ana zaune lafiya da al’umma da kuma kawar da duk wani abu da ya shafi karya doka, ta hanyar haɗa kai da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki wajen cigaban al’umma, inji shi.
A ƙarshe ya yaba wa Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf wajen kishinsa da al’ummar lKano da cigabanta, inda kuma ya jadda cewa a shirye suke wajen ganin buƙatarsu ta biya wajen kawar da matsalar shara ko da kuwa ta hanyar bin ofishin kwamishinan muhalli na Kallno ne, Dakta ɗahiru Muhammad Hashim, yanzu haka kuma batun jin kirin zaɓe ya ce wannan abu na hannun masu ruwa da tsaki na ganin an gabatar da zaɓe lafiya a duk lokacin da aka tafi mu a shirye mu ke a cewar Yusuf Tanko Abdullahi.
