Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, ya bayyana yadda ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ba da gagarumar gudunmuwa wajen ɗaukar nauyin zaɓen gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, a kakar zaɓen 2019.
Dogara, wanda ɗan asalin jihar Bauchi ne da ya riƙe muƙamin shugaban majalisar wakilai daga shekarun 2015 da 2019, ya bayyana hakan ne cikin wani jawabi da ya fitar a ranar Talata, a ƙoƙarinsa na shiga tsakani a musayar yawun da ake tsakanin Wike da Mohammed.
Wannan na zuwa ne a lokacin da dangantakar Wike da Mohammed, ke cigaba da taɓarɓarewa.
Wannan sa-toka-sa-katsin dai ta samo asali ne daga rikicin shugabanci na jam’iyyar PDP tun bayan amincewa da tayin karɓar muƙamin minista da Wike ya yi domin shiga gwamnatin Shugaban ƙasa, Bola Tinubu duk da cewa shi ɗan jam’iyyar PDP ne.
Mohammed, a matsayinsa na shugaban ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP ya ƙalubalanci yunƙurin da Wike ya yi na karɓar muƙamin da bayyana hakan a matsayin cin amana da yunƙurin cika burinsa na ƙashin kai.
A martaninsa, Wike, ya ƙalubalanci cancantar gwamnan Bauchi wajen shugabancin ƙungiyar gwamnonin tare da shawartarsa da ya daina amfani da muƙaminsa na ministan Abuja yana yamaɗiɗi da shi.
Wannan rikici nasu dai na daɗa ya mutsa hazo a tsakanin magoya bayansu.
A ƙoƙarinsa na shiga tsakani, Dogara ya ce Wike, a lokacin yana gwamnan jihar Ribas, shi ne ya samar da taimakon kuɗi da sauran kayan aiki wajen taimaka wa Muhammed domin samun nasarar a zaɓen cikin gida ba tare da neman ya ba shi wani abu ba.
“Ina tunawa gwamna Bala Mohammed cewa a zaɓen cikin gida na gwamna a 2018, ba mu da tabbacin za mu ci saboda abokin hamayyarsa sanata Abdul Ningi, wanda a kan hakan muka nemi taimakon Wike.
“Ni ne na kira Wike na roƙe shi ya sanya baki, kuma ba tare da na gaya masa kai nake roƙa wa alfarma ba. Nan take ya ce idan ba ni da tabbacin kula da komai 100 bisa 100, to na bar masa komai a hannunsa.”
Domin samun nasara a zaɓen cikin gida, Dogara ya bayyana cewa Wike ne ya tsara komai ta hanyar tabbatar da shugaban zaɓen cikin gidan, Dan Orbih, ya isa jihar ta jirgin sama.
“Wike ne ya sanya abokinsa, Chief Dan Osi Orbih, ya zama shugaban kula da zaɓen cikin gida, kuma ya ce na je na tattauna da shi kan duk abin da nake so. A lokacin Chief Dan na garin Benin, kuma haka muka ɗauko shi ya zo jihar.”
Tsohon kakakin majalisar, ya yi iƙirarin cewa ministan ne ya ɗauki nauyin yaƙin neman zaɓensa na gwamna.
Ya ce ya yi mamakin yadda Wike ya ɗauki nauyin zaɓen ba tare da neman a biya shi wani abu ba daga baya.
Don haka, ya ce, gwamnan Bauchi ya yi ƙarya game da batun ɗaukar nauyin zaɓensa:
Dogara ya ce, Mohammed ya samu nasarar zama ɗan takarar gwamnan a jam’iyyar PDP tare da alƙawarin ɗaukar nauyin sauran ‘yan takarar.
Sai dai abin mamaki a lokacin ba shi da kuɗin da zai ɗauki nauyin ‘yan takararsa balle ta sauran ‘yan takara.
“Da farko na ɗauki abin kamar wasa. Amma daga baya na fahimci da gaske ne ya yi mana ƙarya ne game da ƙarfin aljihunsa. Wike ne ya bashi kuɗin da yake buƙata inda ya ba ni hannu da hannu, ni kuma na bai wa Bala.
“Amma daga baya ya amince Bala ya zo ya karɓi kuɗin. Akwai wani hadimin Wike, shi ne ya ba shi kuɗin inda shi kuma Bala cikin murna ya karɓa kamar zai zuba ruwa a ƙasa ya sha. Wannan ne ya ba mu damar fara yaƙin neman zaɓen Bala a jihar Bauchi,” inji Dogara.
“Wannan ba shi ne ƙarshen labarin ba. Amma dai abin mamakin shi ne yadda a bai gindaya kowanne irin sharaɗi a lokacin da ya taimaka wa gwamnan.”
Sai dai mun yi ƙoƙarin jin ta bakin mai taimaka wa Muktar Giɗaɗo domin samun ƙarin bayani kan wannan labari, amma bai amsa kiran wayar ba. Haka ma saƙonnin kar ta kwana da muka tura masa, su ma bai amsa ba.
