Barazanar harin Amurka: Ƙila Trump ya samu taɓin hankali ne, inji Ba’amurken lauya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Antonin sashen tsaro kuma tsohon mai bincike na matakin ƙasa da tarayya a Amurka, wato Ron Filipkowski, ya koka game da abinda ya kira da ‘daidaituwar hankalin’ Shugaba Donald Trump biyo bayan kalamansa na ɗaukar matakin soja akan Nijeriya.

A wani rubutu ta shafinsa na X a ranar Lahadi, Filipkowski ya ce ya dace ace wasu lokutan “mu riƙa la’akari da cewa akwai yiwuwar yana da taɓin hankali.”

Hakan na zuwa ne jim-kaɗan bayan da Donald Trump ya umarci sashen tsaron Amurka ya fara shirin ƙaddamar da hare-hare a Nijeriya sakamakon zargin gwamnatin Nijeriyar da gaza bai wa Kiristoci tsaro da cigaba da kai musu hari.

Saidai, kalaman Filipkowski akan al’amarin ya ta da hazo a Birnin Washington duba da yadda ake cigaba da tafka muhawara a tsakanin masana da sauran jama’a musamman bisa la’akari kasancewar Nijeriya jagora a Nahiyar Afirka ta fuskar tattali da yawan al’umma.

Masu sharhi akan lamuran siyasa sun bayyana ikirarin Shugaban Amurkan na ɗaukar matakin soja akan Nijeriya a matsayin abinda zai shafi al’ummomin ƙasashe da dama.

By Babaji