
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Majalisar Ƙolin Shari’a a Nijeriya (SCSN), ta yi kira ga ɗaukacin al’ummar Musulmi da su fara gudanar da addu’o’in alƙunutu a Masallatai.
A wata takarda da ta fitar ta hannun babban magatakardarta, Nafi’u Baba Ahmad a ranar Laraba, SCSN ta ce ta yi haka ne da nufin samun sauƙin taɓarɓarewar tsaro da ya addabi yankunan Nijeriya da dama da kuma bala’in da ke tunkarar ƙasar daga maƙiyan gida da na waje.
Ta bayyana ayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ake da damuwa akanta da Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi a matsayin shaci-faɗi kuma zalunci.
Haka kuma, ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakin difulomasiyya don bayyana haƙiƙanin al’amarin abinda ke faruwar ga sauran ƙasashen duniya domin samun kyakkyawan fahimta a kai.
A ƙarshe, ta nemi al’ummar Nijeriya da su haɗa kai tare da kauce wa dukkan wani abinda da zai rura wutar gaba da samar da rarrabuwar kai a tsakanin su, lamarin da ka iya zama sababbin kare mutunci Nijeriya a idon duniya.
