Bashin da ake bin Nijeriya ya kai tiriliyan N149 a farkon 2025

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Jimillar bashin da ake bin Nijeriya ya kai Naira Tiriliyan 149.39, bisa ga bayanai daga Ofishin Kula da Bashi na ƙasa (DMO), wanda ya nuna cewa an samu ƙaruwar Naira Tiriliyan 27.72 a bana idan aka kwatanta da Naira Tiriliyan 121.67 da aka samu a 2024.

An samu ƙarin adadin ne sakamakon faɗuwar darajar Naira, wanda hakan ke ci gaba da shafar darajar bashin da ƙasar ta karɓo daga waje.

Dangane da bayanan DMO, bashin da ake bin Nijeriya a waje ya zuwa ranar 31 ga Maris, ya kai Naira Tiriliyan 70.63 kwatankwacin dala biliyan 45.98, wanda ya ƙaru daga Naira tiriliyan 56.02 wato dala biliyan 42.12.

Nijeriya ta karɓi bashi kama daga ƙasashen waje da dama da kuma cibiyoyin kuɗi, ciki har da Bankin Duniya da Bankin Raya Afirka, sai kuma lamunin bankin Eɗim na ƙasar Chana, da kuma wanda ta karɓa daga Japan da sauransu baya ga bashin kasuwanci na Eurobonds da shi ma ta karba.

Haka kuma an samu ƙaruwar basshin cikin gida da gwamnatin kasar da ke Yammacin Afirka ta karɓa, wanda ya kai Naira tiriliyan 78.76 kwatankwacin dala biliyan 51.26, da ta ƙara adadinsu a ƙarshen watan Maris ɗin da ya gabata.

Wannan yana nuna ƙaruwar Naira tiriliyan 14.61 ko kuma kashi 26.1 a duk shekara. A farkon 2025, bashin waje ya ƙaru da kadan daga Naira tiriliyan 70.29 a watan Disambar 2024 – wani ɗan kaɗan ya ƙaru da Naira biliyan 344 ko kuma kashi 0.5.

Sai dai kuma, yayin da bashin dala ya karu da dala biliyan 3.86 a duk shekara, karin girman da aka samu na Naira ya nuna illar da ke tattare da faɗuwar darajar kuɗin ƙasashen waje kan bashin Nijeriya.

Farashin canji na Babban Bankin Nijeriya (CBN) da aka yi amfani da shi wajen sauya bashi a farkon 2024 ya kasance N1,330.26 kan kowace dalar Amurka.

Ko da yake ba a bayyana takamaiman farashin bashin a farkon 2025 ba, giɓin da ke ƙaruwa a cikin Naira yana nuna raunin canjin, wanda kai tsaye ya ƙara wa Nijeriya wajibcin biyan bashin dala da lamunin yuro.

Basusuka na waje sun haɗa da lamuni daga cibiyoyi da yawa kamar Bankin Duniya da Bankin Raya Afirka, hanyoyin haɗin gwiwa, da masu lamuni na kasuwanci, gami da masu saka hannun jari na Eurobond.

Nauyin biyan waɗannan basussuka a matsayin Naira ya ƙara nauyi yayin da kuɗaɗen ƙasar ke ci gaba da zamewa da kimarsu, lamarin da zai iya ƙara zurfafa idan sauye-sauyen da ake yi na daidaita kuɗin bai haifar da sakamako ba.

ɓangaren cikin gida na bashin Nijeriya kuma ya ci gaba da bunƙasa, inda ya kai Naira tiriliyan 78.76 (dala biliyan 51.26) a ƙarshen watan Maris na 2025.

Wannan yana nuna ƙaruwar Naira tiriliyan 13.11 ko kuma kashi 20 daga Naira tiriliyan 65.65 (dala biliyan 49.35) a cikin watan Maris na shekarar 2024. A duk shekara, bashin cikin gida ya karu da Naira Tiriliyan 4.38 ko kashi  5.9, daga Naira tiriliyan 74.38 a watan Disambar 2024.

Gwamnatin Tarayya kaɗai ta samu Naira Tiriliyan 74.89 na wannan jimillar, yayin da Jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya (FCT) a haɗe suka riƙe Naira Tiriliyan 3.87.

By ukarofi