Buhari zai kinkimo bashin N368.7bn daga Bankin Duniya

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya buƙaci Majalisar Dattawa da ta amince masa ya kinkimo bashin Dala miliyan 800 kwatankwacin Naira biliyan 368.7 daga Bankin Duniya.

Buƙatar Shugaban na ƙunshe ne a wata wasiƙa wadda Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya karanto a zauren Majalisar yayin zamanta a rabar Laraba.

Buhari ya ce so yake ya yi amfani da kuɗaɗen wajen shirin kyautata rayuwar ‘yan ƙasa.

Ya ce muddin aka amince masa ya ki kimo bashin, zai raba wa ‘yan Nijeriya mutum miliyan 60 Naira dubu biyar-biyar (N5,000) kowannensu don rage raɗaɗin talauci.

“Majalisar Zartarwa ta Ƙasa ta amince da ciyo ƙarin bashi na miliyan $800 daga Bankin Duniya domin shirin kyautata rayuwar ‘yan ƙasa, don haka nake buƙatar amincewar Majalisar don samun damar aiwatar da shirin a kan kari,” in ji Buhari a cikin wasiƙarsa da ya tura wa Majalisar.

Neman kinkimo bashin na zuwa ne yayin da ya rage kasayda mako uku kafin ƙarewar wa’adin gwamnatin Buhari.