Sanadin sakin matar aure saboda ashana na buɗe gidauniyar tallafin mata – Rabiatu Sa’idu

“Sarautun gargajiya kusan 22 na ke riƙe da su”

Daga ABUBAKAR M. TAHEER 

Hajiya Rabi’atu Umar Sa’idu mace ce mai matuƙar tausayi ga masu rauni. Ita ce mai gidauniyar Sarauniyar Charity Foundation, wanda ta ke ƙoƙari wajen tallafa wa marasa ƙarfi da marayu a kusan ko’ina a faɗin ƙasar nan. Haka kuma ba ta tsaya anan ba, inda ta ke amfani da dukiyarta wajen gina rijiyoyi ruwa a ƙauyukan da ke fama da matsanancin rashin ruwa. Mace ce da ya kamata ta zama allon kwaikwayon duk wani da yake da tausayi kuma yake da ɗan abin hannunshi.  A cikin wannan tattaunawa da wakilin Manhaja, Abubakar M Taheer, ya yi da ita, mai karatu zai fahimci cewa, ba dole sai ka karvo tallafi ga wasu manyan gidauniya ko manyan kamfanoni ko mutane manyan attajirai ne kawai za ka iya bada tallafi ga marasa ƙarfi ba, kaɗan da ka ke da shi, za ka iya kawo sauyi ga rayuwar wani. Haka kuma ta kawo yadda suka yi ƙoƙarin ciyar da mutane dubu hamsin cikin azumin bana, domin samun ladan ciyarwa. A sha karatu lafiya.

MANHAJA: Za mu so ki gabatar mana da kanki ga masu karatunmu.

HAJIYA RABI’ATU: Assalamu alaikum wa rahmatullah. Sunana Hajiya Rabiatu Umar Sa’idu Fulani, wanda kuma ni haifaffiyar Jihar Bauchi ce. Na fito daga gidan sarauta daga ɓangaren mahaifi da mahaifiya. Ina kuma aure a gidan sarauta. Ni ce nake shugabantar gidauniyar Sarauniyar Charity Foundation tare kuma da riƙe da sarautun gargajiya kusan 22. Alhamdulillah, ana zaune da mutane lafiya, ana kuma bada taimako daidai gwargwado.

Yaushe ne ki ka buɗe gidauniyar Sarauniya Charity Foundation?

To Alhamdulillah, ba na mantawa wata rana na dawo gida, sai na taras ana maganar wata mata da ta kawo min ƙarar mijinta ya sake ta kan ashana, gaskiya lamarin ya ɓata min rai, ta yadda za a ce wai kan ashana aka saki mace, bayan kuma ba laifin ta ba ne, ruwan sama ne ya jiƙa wanda aka siya mata, daga nan sai na fara tunanin taimaka wa mata ya zama sun tsayu da ƙafafunsu.

Wannan tasa muka fara bada tallafi ga mutane 50, muka kuma bibiye su cikin hikimar ubangiji sai ya zama abubuwan sun yi albarka.

Wannan tasa na ci gaba da bada irin wannan tallafi. Ya zuwa yanzu mun ɗauki tsawon shekaru goma sha uku da kafuwa, a bana ne ya zama mun sami rijista.

Muna da alƙaluman kusan mata dubu bakwai ne ya zuwa yanzu muka ba su jari, suke ci gaba da gudanar da rayuwarsu.

Kuma kamar koda yaushe, nakan faɗi cewa, ba na neman tallafi daga wurin kowa, hasali ma ni ƴar kasuwa ce, wadda nake harkokina da abinda Allah Ya sa muka samu na ribar kasuwancina, da shi ne nake bada tallafin dama ayyuka na cigaba al’umma.

Ƙungiyoyi da yawa sun sha karrama ki da lambobin yabo kala-kala inda ko a kwanakin baya wata ƙungiya mai duna IAWPA ta baki Jakadiyar Zaman Lafiya da Kawo Cigaba cikin Al’umma. Ko ya lamarin yake?

To Alhamdulillah, kamar dai yadda na faɗa maka tun da farko, ni dai na fito daga gidan sarauta, kuma dama an san sarakai da hidimtawa al’umma, haka kuma ni ce Shugaban Mata Masu Riƙe da Muƙaman Gargajiya ta Nijeriya ( WTTHN) kusan duk ƙungiyoyin da suke bada lambar yabo sukan ɗauki wani ɓangare ne da nake bada tallafi sai su ga ya kamata ace sun karramani, domin ƙarfafawa da kuma jawo hankulan masu hannu da shuni wajen gudanar da makamancin wannan aiki na alkairi. Babu abinda za mu ce musu sai dai godiya da kulawa da suke bamu.

Waɗanne nasarorin ne za a ce an samu zuwa yanzu?

To a gaskiya nasarori dai ba ma za su ƙirgu ba, wasu daga ciki su ne; mun gina rijiyoyin bohol guda dubu uku da wani abu a faɗin ƙasar nan. Haka kuma akwai marayu kusan dubu biyu da nake ɗaukan nauyin su.
Haka kuma mun gina masallatai guda xari biyar da uku a faxin Arewacin qasar nan. Haka kuma kafin Ramadan, mu kan ciyar da makarantun tsangaya. Mukan ba su abinci da za su ci tsawon sati guda. Kusan almajirarai dubu biyu da ɗari biyar muka hana bara. 

Haka kuma nakan tallafa wajen raba magunguna kyauta ga marasa lafiya duk don cigabantar da al’umma gaba.

Na kan shiga lungu da saƙo, wani lokaci na kan yi dogon zango a ƙasa, domin shiga ƙauyukan da muke bada ita.

A cikin Ramadan ɗin nan da ya gabata, mun ga wasu ayyukan ciyar da masu azumi da ki k yi. Za mu so ki mana ƙarin haske kan lamarin.

To Alhamdulillah, a cikin watan da ya shuɗe, watan alfarma, Ramadan, mun yi wani ƙudirin na ciyar da al’umma masu azumi a jihohin Arewa goma sha tara, inda mukan bada abinci mai kyau. Kusan kowa na da kalan abinci guda biyar wanda kusan bayin Allah dubu hamsin suka amfana.

Sai dai akwai bambanci a jihohi Kebbi da Zamfara da Abuja, kusan mutane ɗari biyar zuwa dubu ɗaya mukan ciyar a kullum a wasu jihohi duba da yanayin mutanen da ke yankin.

Kuma zan iya cewa, masu azumi da yawa sun ji daɗin wannan agaji, duba da yanayin da ƙasar ta ke ciki na matsin tattalin arziki. Babu abinda za mu ce ma Allah sai dai godiya, domin ba yin mu ba ne.

Waɗanne ƙalubale ne za a ce ana fuskanta a wannan aikin na tallafa wa bayin Allah?

To a gaskiya ƙalubalai kan an fuskance su, dama babu abinda za ka yi a rayuwa ya zama babu ƙalubale a ciki. To amma, babban maganinsa shi ne haƙuri, kuma ba lalle sai na fito na bayyana su ba, an dai wuce gun.

Da wane abu ki ke so a tuna ki ko bayan ba ranki?

To Alhamdulillah, Ina son ko Ina raye, ko Ina mace a rinƙa tunani a matsayin mace mai ƙoƙarin yin aikin alheri ga al’umma.

Sannan ba ma tunawa kawai ba, Ina buƙatar a min addu’a, misali, ka ɗauki iya Jihar Kano, muna da rijiyoyin bohol ɗari hudu da sha biyar. Za ka ji bayin Allah suna ta addu’a, suna amfana da wannan ruwa da aka samar musu. Kuma kaga tsawon lokaci da wannan rijiyoyin suke nan ana rubuta min lada. Iya wannan ya ishe ni abin jin daɗi. Ina kuma fatan Allah Ya karɓi ɗan kaɗan ɗin da muke aikata wa wajen hidimtawa al’umma.

Wane kira ki ke da shi ga masu hannu da shuni wajen tallafa wa al’umma?

To Alhamdulillah, kira na gare su shi ne, waɗanda suke da halin taimaka wa, su taimaka, koda makusantansu ne, haka kuma mutum ya sani, ba wai ance duk dukiyar ka za ka bada ba. A’a koda kashi ɗaya ce cikin ɗari ka ɗauka ka tallafa wa wanda Allah bai hore musu ba. Za ka ji daɗi a ƙashin kanka, haka su ma za su ji daɗi, ga uwa uba tarin lada a wurin Allah.

Mun gode.

Ni ma na gode ƙwarai da gaske.