EFCC ta tsare tsohon Ministan Lantarki, Sale Mamman kan zargin karkatar da N22bn

Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa da Zambar Kuɗaɗe (EFCC), ta tsare tsohon Ministan Lantarki, Sale Mamman, kan zargin nasabarsa da almundahanar Naira biliyan 22.

An tsare Mamman ne da safiyar ranar Laraba.

Mamman ya riƙe muƙamin Ministan Lantarki a ƙarƙashin gwamnatin Muhammadu Buhari daga 2019 zuwa 2021.

Tsare Mamman ya taso ne sakamakon binciken da hukumar ke yi kan batun aiwatar da wasu ayyuka ƙarƙashin Ma’aikatar Lantarki.

Ana zargin Mamman da haɗa baki da jami’an Ma’aikatar masu kula da sashen kuɗi na ayyukan lantarki a Zungeru da Mambilla wajen karkatar da kuɗi Naira biliyan 22 wanda suka raba a tsakaninsu.

Kazalika, binciken ya bankaɗo kadarori na miliyoyin Naira da Dala a Nijeriya da ƙetare waɗanda aka danganta su da waɗanda ake zargin.