Daga AISHA ASAS
Kawo yanzu, jama’a da dama na tsumayar jana’izar Babban Hafsan Sojoji, Ibrahim Attahiru, wanda za a gudanar a babban Masallacin Abuja.
Manyan jami’an soja 6 ne za a yi wa Sallar Jana’izar waɗanda suka rasu sakamakon hadarin jirgin sama da ya rutsa da su a Kaduna.

Yayin da ragowan sojojin za a binne su ne daidai da tsarin addininsu na Kirista.