Rasuwar Attahiru babban ibtila’i ne ga ƙasa – Magashi

Daga UMAR M. GOMBE

Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi, ya ce abin kaɗuwa ne ainun rasuwar da Babban Hafsan sojoji na 21, Lt General Ibrahim Attahiru, ya yi a haɗarin jirgin sama kimanin watanni huɗu da naɗa shi kan sabon muƙaminsa.

Cikin saƙon ta’aziyyar da ya miƙa, Janar Magashi ya ce haɗarin jirgin wanda ya yi ajalin Attahiru da sauran jami’an da suke tare, babban ibtila’i ne ga ƙasa.

Ministan ya miƙa ta’aziyyarsa ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da Rundunar Sojoji da iyalan mamatan da ma ƙasa baki ɗaya dangane da wannan babban rashi da ya auku.

Magashi ya bayyana marigayi Attahiru a matsayin gwarzo wanda ya yi wa ƙasarsa aiki bilhaƙƙi a halin rayuwarsa, inda ya yi aiki a wurare da dama da kuma riƙe muƙamai daban-daban.

Ya ce marigayin ya samu zarafin jan ragamar rundunar sojoji ta ƙasa a lokucin da ya dace don yaƙi da matsalolin tsaron ƙasa, sai ga shi bai yi nisan kwana ba a kan muƙamin inda ya kwanta dama.

Ya ci gaba da cewa, Nijeriya ba za taɓa mancewa da gudunmawar da marigayin ya bayar ba wajen ganin ƙasa ta cigaba yadda ya kamata.

A ƙarshe, Ministan ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayi Ibrahim Attahiru Ya sanya Aljanna Firdausi ta zama makomarsa. Tare da fatan Allah ya bai wa ƙasa, rundunar sojoji da iyalan marigayan haƙuri da danganar wannan rashi.