Bayan jagorantar Nijeriya a Olympics, FIBA ta zaɓi Wakama a matsayin wacce ta fi iya horarwa

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

An zaɓi mai horar da ƴan wasan ƙwallon kwando na mata (DTigress), Rena Wakama a matsayin wacce ta fi nuna bajinta a gasar Olympics da aka yi a Farisa, babban birnin ƙasar Faransa.

DTigress ta taka rawar gani a ranar farko bayan doke Austaraliya da ta yi wanda shi ne karo na farko da ta samu nasara a zangon rukuni-rukuni.

Bayan kwanaki kaɗan ne ƙungiyar ta sake yin nasara bayan da ta doke Canada wanda hakan ya sa ta zama ƙasar Afirka ta farko da ta yi nasara sau biyu a jere inda a sanadiyyar haka ne ta kai matakin ƙalubale.

Sannan hakan ya sa ta zama ƙungiyar Afirka ta farko da ta kai matakin wasan daf da na kusa da na ƙarshe a ɓangaren mata ko maza a kowane wasa na Olympics.

Sai dai duk da ƙoƙari da bajintar da DTigress ta nuna, haka bai sa ta yi nasara ba a karawar ta ƙungiyar ƙasar Amurka.

By Babaji