Sanatoci sun musanta zargin da Obasanjo ya yi na kiran su shaiɗanu

Spread the love

Sanatocin Nijeriya sun musanta zargin da tsohon shugaban ƙasa Obasanjo ya yi, ya na cewa su da kansu su ke sanya ma kan su albashi.

Sanatocin sun musanta wannan da cewa ba haka abin yake ba, akwai hukumar da ke lura da wannan kamar yadda doka ta zayyana. Wannan zargin ya fito ne bayan wasu ƴan majalisu sun kai wa Obasanjo ziyara a gidan shi.

A wata sanarwa da mai magana da yawun sanatocin ya fitar, Sanata Yemi Adaramadu, ya bayyana wannan a mastayin labarin ƙanzon kurege da ba shi da tushe. Ya ce wannan wata maƙarƙashiya ce ga ‘yan majalisun.

Ya cigaba da cewa, babu wani ɗan majalisa da ke samun wani alfarmar kuɗi daga shugaban ƙasa.

Duk wani kuɗi da a ke biyan su, kuɗi ne da doka ta bada dama a biya.

Sanatan ya umarci duk wani wanda ya ke da wani shaida saɓanin abinda ya faɗa to ya fito ya bayyana shi. Don haka yace abinda a ke faɗa cewar mu shaiɗanu ne, ba gaskiya a ciki.

By ukarofi