Bayan shekara shida a tsare, kotu ta yanke wa ɓarayin da suka yi sata a Offa hukuncin kisa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Mai Shari’a Haleemah Salman ta babbar kotun tarayya da ke Jihar Kwara ta tabbatar da waɗansu mutane biyar da hannu a laifukan mallakar malamai ba bisa ƙa’ida ba da fashi da makami da kuma kisan kai, inda ta ce hukuncin waɗannan laifuka shi ne kisa.

Lamarin ya auku ne a watan Afrilun 2081 inda ta ce baki ɗaya hujjojin da aka gabatar a kan su sun tabbatar da cewa mutanen su na da hannu dumu-dumu acikin laifukan.

Mutanen sune; Ayoade Akinnibosun, Ibikunle Ogunleye, Adeola Abraham, Salahudeen Azeez da kuma Niyi Ogundiran.

A lokacin da ya ke ganawa da manema labarai, lauyan da ke kan batun ya ce matsalar annobar COVID-19 da wasu ayyuka a mataki na ƙasa da alƙalin ta fuskanta su suka sanya aka samu jinkiri game da kammala shari’ar, ya na mai godiya gare ta kan hukuncin da ta yi.

Saidai, ɓangaren da ke kare masu laifukan sun ce za su ɗaukaka ƙara nan ba da jimawa ba.

Hakan na zuwa ne shekaru shida bayan wasu ɓarayi sun kai hari a yankin Offa na Jihar Kwara inda suka yi fashi a bankuna biyar da ke garin.

A sanadiyyar haka aka rasa rayuka da dama ciki harda jami’an ƴan sanda guda biyu tare da sace maƙudan kuɗaɗe wanda hakan ya haifar da zaman ɗar-ɗar acikin al’umma.

By Babaji