
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ganawa da zaɓaɓɓen gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo a Fadar shugaban ƙasa da ke Abuja yayin da ya karɓi baƙoncinsa.
Okpebholo ya je fadar ne tare da wasu gwamnonin jami’yyar APC da suka haɗa da; Shugaban tawagar gwamnnonin (PGF) kuma Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma; Shugaban gwamnonin Nijeriya (NGF) kuma Gwamnan Jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazak; Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna; Gwamna Usman Ododo na Jihar Kogi da kuma Gwamna Dapo Abiodun na Jihar Ogun.
Sauran sune; Sanata Adams Oshiomhole da kuma Mataimakin gwamnan Edo Mista Philip Shaibu.
Hukumar zaɓe (INEC) ta sanar da Monday Okpebholo a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen gwamnan Edo da aka yi a ranar Asabar da ta gabata.
