
Daga UMAR GARBA a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta ce, ɗalibai 29,633 daga jihar sun samu nasarar lashe kiredit 5 zuwa sama, ciki harda darasin Lissafi da Turanci a jarrabawar NECO ta shekarar 2024.
Kwamishinar Ilimi, Zainab Musa Musawa ce ta bayyana hakan yayin da ta ke zantawa da manema labarai a birnin Katsina.
Ta ce, alƙaluman da hukumar shirya jarabawa ta NECO ta fitar, ya nuna cewa Katsina ce jiha ta shida a jerin jihohin Nijeriya wajen samun sakamako mai kyau.
“Wannan babbar nasara ce, inda ɗalibai 29,633 suka cika wannan muhimmin ma’auni a cikin jihohi 30 har da babban birnin tarayya Abuja”, inji ta.
Musawa ta ƙara da cewa ɗaliban da suka yi nasarar daga Katsina sun isa su cike guraben da jami’o’i ke ware wa ɗalibai da sauran manyan makarantun gaba da sakandare na shekarar 2024 zuwa 2025.
Musawa ta ce, wannan adadi ya nuna an samu gagarumin ci-gaba idan aka kwatanta da ɗaliban da suka zauna jarabawar su kimanin 25,152 a shekarar 2023, wanda ke nuna ci-gaban da aka samu ya kai kusan kashi 17.8 cikin ɗari.
“Gwamnatin Gwamna Dikko Raɗɗa, wanda shi kansa tsohon malami ne, ta taka rawar gani wajen magance ƙalubalen da ake fuskanta a fannin ilimi, waɗanda yawancin su an gada ne daga gwamnatocin baya.”
“Bayan hawansa mulki, Gwamna Raɗɗa ya kafa tarihi tare da ɗaukar malamai 7,325 aiki a cikin watanni uku kacal na gwamnatinsa”, inji Kwamishinar.
