Daga IMRAN ADAMU
Masu iya magana dai kan ce, “Zakaran da Allah Ya nufe shi da cara, ko ana muzuru ana shaho sai ya yi”.
Zabbaben Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Benjamin Kalu yana kan kafa tarihi na zama fitacen dan siyasa da duka jam’iyyun siyasa ke alfahari da nasarar da ya samu.
Duba ga rayuwar Hon. Kalu a majalisa ta Tara (9th Assembly) ne farkon shigowarsa majalisa a matsayin zaɓaɓɓen ɗan Majalisa da ke wakiltar mazaɓarsa ta Bende Federal Constituency daga Jihar Abia, amma hakan bai sa ya yi sanyin jiki a harkar majalisar da ta gabata ba wato ta Tara. Saboda ya samu nasarori masu tarin yawa, wanda suka hada da zamansa na mai magana da Yawun Majalisar, kuma Shugaban Kwamitin Yada Labarai na Majalisar.
Duk da yamutsi da rashin jituwa da aka samu a takarar kujeran Kakakin Majalisa a watannin baya, Benjamin na daya daga cikin ‘yan takarar kujerar, amma saboda halacci da biyyeyya ga jami’arsa ta APC, Hon. Kalu yana sahun gaba na wadanda suka fara janye takara wa Hon. Tajjuddeen Abbas (Iyan Zazzau) domin samun daidaito a nasarar jam’iyya.
Takwas ga Watan Mayu a shekarar nan ne Fadar Sabon Zabbabben Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya fitar da Sanarwan Zaben Hon. Tajjuddeen Abbas mai wakiltan Karamar Hukumar Zariya a majalisar tare da Hon. Benjamin Kalu a matsayin ‘yan Takarar Shugabancin Majalisar da Shugaba Bola Tinubu ya yi na’am da takararsu. Lamarin da ya tada hazo a kafofin sada zumunta da ma gidajen Jaridu da Yada Labarai na kasa bakidaya! Amma duk da haka Hon. Benjamin kalu bai sa ya samu abokin adawa ba a takararsa na Mataimakin Kakakin Majalisar.
Hon. Kalu ya yi nasara ba tare da wani ko wata sun yi hamayya da takararsa ba, A hasali ma shi kadai ne ke takara a ranar da aka gudanar da zaben Sugabancin Majalisar.
Sai dai ana wata ga wata, duk da nasarar Hon. Benjamin Kalu na zama mataimakin Kakakin Majalisa, akwai kalubale da yake fuskanta a gaban Kotu, inda ake tuhumar ingancin nasarar zabensa na Dan Majalisa mai wakiltar Mazabar Bende Federal Constituency.
Mataimakin Kakakin Majalisar Hon. Kalu ya yi Nasara A Kotu:
Kotun Sauraren ƙararrakin zabe dake zama a Umuahia, Jihar Abia, Ta Tabbatar da Nasarar Zaɓen Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Benjamin Okezie Kalu.
Kotun dai ta yi fatali da karar da dan Takarar jam’iyyar Action Alliance (AA) Ifeanyi Igbokwe ya shigar, wanda ya kalubalanci Nasarar Kalu.
Kotun ta yanke hukuncin cewa Kalu ya bi tsarin da ya dace don tabbatar da sunansa, don haka karar ba ta da tushe balle makama. Wannan shi ya baiwa Hon. Kalu tabbacin zama mataimakin Kakakin Majalisar wakilai a wakilci na 10.
Mutane da dama na ganin Hon. Kalu a matsayin dan kishin kasa, kuma mai hanzari da hazaƙa wajen inganta shugabanci ba ma a Najeriya ba, a Nahiyar Afirka bakidaya.
Imran ya rubuto ne daga Abuja. A na iya samun sa a wannan adireshinsa na imel; [email protected]