BESDA: Gwamna Lawal ya jagoranci tawaga zuwa taron bita a Rwanda

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jagoranci tawaga ta musamman zuwa Kigali don taron bita na yini huɗu a matsayin ɓangare na kammala shirin ba da nagartaccen ilimi na Better Education Service Delivery for All (BESDA) a jihar.

Bitar mai ƙunshe da ayyuka daban-daban, an soma ta ne daga ranar Litinin, 4 ga Disamba, da zummar farfaɗo da fannin ilimin Jihar Zamfara.

Mai magana da yawun Gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana a cikin sanarwar da ya fitar cewa, shirin BESDA shiri ne na Bankin Duniya wanda aka ƙirƙiro da nufin bunƙasa sha’anin ilimi da kuma bai wa yaran da suka daina zuwa makaranta damar samun ilimi a Nijeriya.

Sanarwar ta ƙara da cewa, shirin BESDA na da burin inganta sha’anin ilimi da kuma ƙarfafa aiki da gaskiya a jihar ta Zamfara.

A cewar Idris, “Daidai da ayyana dokar-ta-ɓaci a fannin ilimin Zamfara, Gwamna Dauda Lawal ya jagoranci tawaga da ta ƙunshi Sakataren Gwamnatin Jihar, Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha, Shugaban Hukumar UBE na Zamfara da sauransu zuwa taron bita a ƙasar Rwanda.

“Majalisar Ɗinkin Duniya ta shirya bitar ne a matsayin ɓangare na shirinta na Better Education Service Delivery for All (BESDA).

“Shirin da ke da manufar rage yawan yaran da suka daina zuwa makaranta a Nijeriya wanda a halin yanzu, ita ce matsala mafi girma a duniya in ji UNESCO.

“A tattaunawar da suka yi da Ma’aikatar Ilimi ta Rwandan, tawagar Jihar Zamfara ta koyi dabaru da matakai da sauran shiryen-shiryen da za su taimaka wajen magance matsalar jinsi a makarantu,” in ji Bala Idris.

Kazalika, ya ce tawagar ta kuma ziyarci wasu zaɓaɓɓun makarantun gwamnati a wajen Kigali domin kalato dabaru da tsare-tsaren da za su amfani tsarin bayar da ilimi a faɗin Jihar Zamfara.