Harin bom: Shettima ya ziyarci Kaduna don jajanta wa al’ummar Tudun Biri

Daga BASHIR ISAH

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya ziyarci Jihar Kaduna domin jajanta wa ‘yan uwan waɗanda harin bom da sojoji suka kai bisa kuskure ya rutsa da su a yankin Tudun Biri a jihar.

Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani da sauran manyan jami’an gwamnati ne suka tarbi Mataimakin Shugaban Ƙasar bayan da ya sauka a barikin sojojin saman da ke Mando.

Tawagar da ta yi wa Shettima rakiya zuwa Kaduna a ranar Alhamis ta ƙunshi Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajuddeen, Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar; Shugaban APC na Ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje da dai sauransu.

Ziyarar Shettima na zuwa ne kwana huɗu bayan harin da ya laƙume gomman mutane da tare da jikkata wasu dama a Tudun Biri.

Tun bayan aukuwar harin a ranar Lahadin da ta gabata, Rundunar Soji ta ta ɗauki alhakin aukuwar lamarin, inda ta ce hakan ya faru ne bisa kuskure.