BIDIYO: Zanga-zangar NLC a Abuja

Daga BASHIR ISAH

Kamar yadda ta sha alwashi, Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC), ta fara gudanar da zanga-zangar a sassan ƙasa.

A Babban Birnin Tarayya, Abuja, an ga mambobin ƙungiyar sun mamaye ƙofar shiga Babbar Kotun Tarayya da ke birnin.

NLC ta bakin shugabanninta, ta ce ta ɗauki wannan matakin ne domin nuna rajin jin daɗinta kan tsadar rayuwar da ‘yan Nijeriya ke fuskanta a sakamakon cire tallafin mai.

Don haka take buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakan da za su sanyaya wa ‘yan ƙasar ƙuncin rayuwar da suke fuskanta haɗi da sauran buƙatun ƙungiyar.

Kalli bidiyon cuncurundon da mambobin NLC suka yi a Abuja:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *