“Ya kamata a bar talaka ya numfasa”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A wani bidiyo da ake yaɗawa ta kafafen sada zumunta, an nuna Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu cikin wani jawabi da ya yi cikin harshen Turanci, a lokacin yaqin neman zaɓe yana ambata cewa, ya kamata a bar talaka ya numfasa!

A lokacin shi ma da kansa ya nuna tausayawa ga halin da talakan ƙasar nan ke ciki, don haka yake kwaɗaitarwa ‘yan Nijeriya cewa, a ƙarƙashin gwamnatinsa za a samu walwalar rayuwa, har a dara. Kuma a kan haka talakawan ƙasar nan mafiya rinjaye suka zaɓe shi, bisa tunanin idan ya hau mulkin ƙasar nan za a samu sassauci, rayuwa za ta yi sauƙi.

Wannan shi ya sa da dama ‘yan Nijeriya suka shiga ruɗani da mamaki yayin da suka ji cikin jawabinsa na karvar mulki yana sanar da cire tallafin man fetur. Abin da tun a gwamnatocin baya aka yi ta taƙaddama a kai, kuma ’yan Nijeriya suka yi ta bore don nuna qin amincewa a kan cire wannan tallafi da ake bai wa harkar shigo da man fetur.

Domin kuwa kamar yadda muke gani a halin yanzu wannan janye tallafin man fetur ya jefa rayuwar miliyoyin ’yan Nijeriya cikin halin ƙaƙa-ni-kayi, saboda yadda farashin komai ya tashi a ƙasar nan, saboda ƙaruwar farashin mai.

A jawaban da jami’an gwamnati da masu goyon bayan cire tallafin man suka riƙa yi a baya shi ne cewa wannan tallafi wasu ’yan tsiraru ne suke morarsa ba talakawa ba, amma yanzu da aka cire mun fahimci irin gatan da tallafin yake yi wa rayuwar ’yan Nijeriya.

Duk da ƙalubalen da ake fuskanta yanzu an fahimci cewa tallafin da gwamnati ke biya na maqudan kuɗaɗe ba kawai zurarewa yake yi zuwa aljihun wasu ’yan tsiraru ba, yana ma zama katangar da ‘yan ƙasa ke jingina da ita suna samun tallafin rayuwa a fakaice.

Har ta kai a yanzu talakawan da masu fashin baƙi na ganin gara ma a dawo da cigaba da biyan wannan tallafi, domin a samu sauƙin tsadar rayuwa. Duk kuwa da alƙawarin da Gwamnatin Tarayya ta yi na cewa, za a raba wa al’ummar ƙasa wani tallafi na kayan abinci, takin zamani da motocin sufuri masu sauƙin kuɗi da kuɗaɗen jari ga qananan ‘yan kasuwa, ’yan Nijeriya na ganin ko da hakan ta samu, babu wani abu da zai sauya, domin kuwa tallafi ne na wani lokaci ƙalilan, kuma ba kowa ne zai samu ba. Jama’a sun dawo daga rakiyar hukumomi, ba su da ƙwarin gwiwa kan cewa, gwamnati za ta fitar da wani tallafi da har zai kai gare su, a yadda ta ambata ba.

Duba da warwason da wasu suka riƙa yi a shekarun baya kan irin waɗannan haƙƙoƙi na tallafi da aka an bayar. Musamman ma da aka ce gwamnonin jihohi ne za a bai wa alhakin isar da kuɗin nan ga jama’ar jihohinsu, alhalin talakawa sun san yadda irin wannan kasafi yake kasancewa, sai na kusa da gwamnati, ’yan jam’iyyar gwamnati mai mulki, ‘yan korensu, da makusantansu kawai suke samu su dangwala.

A wasu wuraren ma kashe mu raba a ke yi, kamar a inda aka ce a bayar da duba takwas da ƙyar dubu uku ko huɗu ke isa hannun talaka, saboda waɗanda aka bai wa alhakin rabon sun yagi rabonsu. Wanne sassauci hakan zai kawo wa talaka? Ta yaya ’yan Nijeriya za su gasgata alƙawarin gwamnati a kan abin da ya shafi rabon tallafin kuɗi ko na abinci?

Bisa ga dukkan alamu dai da ƙyar talakan ƙasar nan zai samu damar numfasawa, biyo bayan alƙawarin da gwamnatin tarayya ta yi na cewa, babu batun mayar da hannun agogo baya kan al’amarin tallafin man fetur. Sai dai gwamnati da al’ummar ƙasa su samo wasu dabarun na cigaba da rayuwa cikin sabon yanayin da aka samu kai.

Tambayar da wasu ’yan Nijeriya ke yi shi ne, me zai hana gwamnati ba za ta yi amfani da kuɗaɗen da ta ce ta janye su daga tallafin man fetur, zuwa ga wasu ayyuka na raya ƙasa ba? Suna nufin kenan gwamnati ta kafa wani asusu na inganta walwalar ’yan Nijeriya, kamar misalin Asusun Rarar Man Fetur na PTF da tsohuwar gwamnatin marigayi Janar Sani Abacha ta samar, lokacin da aka samu riba daga cinikin ɗanyen man fetur da gwamnatin ƙasar nan ke yi.

Babu shakka da za a yi haka, ba ƙaramin canji za a samar ba, abubuwa za su yi sauƙi, har ma talaka ya fito da bakinsa yana cewa gara ma da aka cire tallafin man, don ya ga sakamakon yadda gwamnati ta sarrafa kuɗaɗen da ake adanawa, don amfanin ’yan qasa. Amma da ƙyar a ce hakan ta samu, saboda ko kaɗan ba a ma waiwayi wannan ɓangaren ba, kuma har yanzu ba a ce ga abin da ake yi ko za a yi da kuɗin ba.

Ba ni kaɗai ba, da dama daga cikin masharhanta da masu nazari kan tattalin arzikin ƙasa, na ganin tsare-tsaren da gwamnati ke fitowa da su na inganta tattalin arziki su ne suke ƙara jefa talakawan ƙasar cikin ƙuncin rayuwa a maimakon sassauta halin rayuwar da suke ciki.

Kamar yadda na rubuta a makon da ya gabata, kowacce gwamnati ta shigo tana zuwa ne da alqawarin daidaita al’amura, amma ita ma da ta hau, sai ka kasa gane ina ta dosa. A maimakon a toshe ƙofofin da ake samun damuwa, sai ka ga kullum damuwoyin qara yawa suke yi.

Ko a ƙarshen makon da ya gabata ma sai da sai da aka rawaito tsohon shugaban qasa Olusegun Obasanjo ya na faɗa a wajen wani taron ƙaddarar da littafin da wani tsohon minista ya wallafa, inda ta cikin bidiyon da aka kunnawa mahalarta taron, aka jiyo tsohon shugaban ƙasar yana bayyana takaicinsa game da yadda wasu tsare-tsaren gwamnati ke haifarwa ƙasar nan koma baya, saboda da rashin kiyaye ƙa’idojin aiwatar da su.

Sakamakon halin da ma’aikatan gwamnati da sauran ‘yan Nijeriya suka shiga biyo bayan tsadar rayuwa da aka shiga, haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa ta NLC ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin zuwa ranar 2 ga watan Agusta mai zuwa ta tabbatar ta janye sabon tsarin da ta ɓullo da shi na ƙarin kuɗin ma har sau biyu cikin wata guda, ko kuma ƙungiyar ta jagoranci yajin aikin ƙasa baki ɗaya, har sai abin da hali ya yi.

Sai dai kuma ba lallai ne wannan barazana ta ƙungiyar NLC ta yi tasiri ba, saboda Gwamnatin Tarayya dai ta ce babu sauyi, kuma da alamun ba za ta lamunci yajin aikin ƙasa baki ɗaya ba.

Wani mai zanen barkwanci, ya zana hoton shugaban ƙasa Tinubu, ya daddage yana ta wankin matsalolin Nijeriya, sai aka nuna ya murɗe talaka yana ta matse shi kafin a ɗauraye.

Abin da ke nuna cewa tsare tsaren wannan gwamnati talaka kawai suke quntatawa. Muna fatan gwamnati da muƙarrabanta za su sake zama su duba waɗannan ƙorafe-ƙorafe, don su kawo gyaran da zai amfani kowanne ɗan Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *