Bincike da karatu suka sa ake min kallon ba ’yar Arewa ba – Maryam Bichi

“Nasara ce yadda mutane ke kallo na a matsayin mafita ga al’umma”

Daga MUHAMMADU MUJITTABA, a Kano 

Matashiya Maryam Bichi, ‘yar gwagwarmaya akan ilimin kasuwanci da fasahar sadarwa da bunƙasa kasuwancin zamani ta hanyar ilimantar da al’umma maza da mata da burinta na zama tauraruwa daga matan Arewa da ta kafa makarantar fasahar sadarwa a rayuwarta da dai sauran bayanai masu mahimmanci na ƙalubale da nasarorin da ta samu a rayuwarta ta shekaru 29 a duniya. Wakilinmu ya samu zantawa da matashiyar, don haka ku biyo mu don jin yadda tattaunawar ta kasance.

MANHAJA: Za mu so mu ji wacce ce Maryam Bichi a taƙaice?

MARYAM BICHI: To ni dai kamar yadda ka faɗa sunana Maryam Abbas Abdulƙadir Bichi, wacce aka fi sani da Maryam Bichi. An haife ni a watan Yuni na shekarar 1994, kuma ni ‘yar asalin Ƙaramar Hukumar Bichi ce, da ke Jihar Kano. Na fara makarantar Norther ne a Legos, daga nan na fara makarantar firamare a garin Abuja tsakiyar Najeriya, sakamakon shi mahaifina ma’aikacin banki ne, to sai aka dawo da shi Kano, inda a nan ne na kammala firamare, ta Gwamnatin Tarayya F.G.C da ke Kano. Daga nan ne kuma na wuce makarantar ‘yan mata da ke garin Bebeji, wato Bebeji Government Girls secondary School ta Kano Foundation inda na kammala tare da sauke karatun Al’ƙur’ani mai girma duk dai a lokaci guda.
To daga nan ne kuma sai na tafi kwalejin share fagen shiga jami’a da aka fi sani da CAS, inda na yi shekara guda. Daga nan ne kuma na wuce jami’ar KUST a wancan lokacin kenan, wadda a yanzu ta koma ADU, wato Aliko Ɗangote University. Na shiga a shekarar 2012, inda na karanta Tarihin Ƙasa, wato Geography a turance. Kuma da taimakon ubangiji na fita da kyakyawan sakamako wanda na bar tarihi mai yawa a Jami’ar ta Ɗangote musamman ganin na riƙe muƙamai daban-daban, tun daga kan sashin mu na Geography har ma abin da suka shafi jami’ar bakiɗaya na daga ƙungiyar ɗalibai da kwamitin zaɓuɓɓuka na ƙungiyar ɗalibai a wancen lokacin. Na kammala jami’ar ne a 2016 inda na tafi bautar ƙasa NYSC a jami’ar gwamnatin tarayya da ke Dutse da ake kira FUD da ke Jihar Jigawa. 

Na samu takardar shaidar fasahar sadarwa Digital Market da kuma ayyuka a wurare daban-daban da muqƙamai daban-daban kamar ma’aikatar KANGES, L&Z da sauransu.
Haka kuma na yi difloma akan kimiya fasaha da kuma karance-karance da kwasa-kwasai da dama musamman abin da ya shafi fannin sadarwa da sauransu. Na kuma yi makarantar koyan sana’ar da ake ce ma ta AHIP, haka kuma na yi karatu a Cibiyar Kula da Tallace-Tallace ta Ƙasa, wato AFCON wadda yanzu haka ni mamba ce a AFCON kuma yanzu haka ina karata harkar kasuwanci zamani a makarantar DBS, wato Ɗangote Business Studies da ke BUK jami’ar Bayero Kano, da dai sauransu.

Yanzu wane matsayi Maryam Bichi ke ciki a halin yanzu?

To a halin yanzu dai ni ce shugabar kamfani mai inganta Digital Concept. Wannan kamfanin wanda aikin sa shi ne, zamanantar da sana’oin mutane, kuma ni ce na jagoranci taron bunƙasa sana’oi mu a tsarin soshiyal midiya wanda daga baya aka fara taron a fili ido na ganin ido a doran ƙasa bayan Korona a 2020 inda na farko wanda ya samu halartar ‘yan kasuwa matasa maza da mata domin wayar da kansu da bunƙasa sana’oinsu a wannan lokacin.

Kasancewar ki matashiya ‘yar Arewa, ya aka yi ki ka yi irin wannan tunanin ko in ce menene silar wannan harkar kasuwancin zamani ta fuskar sadarwa?

to ina ganin haka Allah ya tsara domin ni na faɗa maka a baya na yi siyasar makaranta inda har na yi shugabar ƙungiyar ɗalibai ta sashin mu na Geography a jami’ar na kuma shiga ƙungiyoyin matasa don kawo cigaba a kaina da al’umma ta da ƙasa ta. Baya ga haka, ni mai bincike ce da sha’awar karatu har ake ganin ni ba yar Arewa bace saboda yadda nake magana da Turanci da makamantan su. 

Wannan kallo da ake mun sai ya zamemin babban alkhairi ta hanyar sanin kishin Arewa da kishin al’ada ta Arewa da harshena na Hausa da rie sharia ta addininmu tun da ina so ni in zama tauraruwa daga Arewa wadda ta san ƙanƙame harshena, al’ada da addinina, domin in zama abin koyi ga waɗanda za su biyo bayana ko kuma waɗanda muke tafiya tare, kuma shi ne ya sa suka sa lamurana na rubuce-rubuce a soshiyal midiya ko a wani taro da ni zan shirya ko na ke da tacewa to da Hausa ake gabatarwa dan kishin harshe na da al’ada ta da shari’a ta kamar yadda na shaida maka a baya kuma duk shiga ta sai ta nuna daga Arewa na ke.

Yayin da ki ka yi wannan ƙudiri ko ki ka yanke shawarar fitar da Arewa a dukkan sha’anin ki, ko yin hakan ya zo da wasu ƙalubale?

Tabbas wannan abu da na sa kaina ya zo da ƙalubale domin akwai surutai masu yawa da na ke samu, musamman da ake ganin irin wannan gwagwarmaya da faɗi tashi na mata musamman kamar matashiya za ai ta maka kallo da surutai daban-daban da za a ta kwatan ta ka kamar wani abu ne da ka zama mai tasiri akan al’amuran fasahar sadarwa ana kallon ka a matsayi ɗan ‘social media’ da za a baka fasara wacce aka gadama, kuma ƙalubalen ya zama kashi biyu, na farko tsakanin ka da iyayen ka da al’ummar ka kaga ƙalubale na cikin gida kenan wannan tasa duk wani abu da zan yi na ba daidai ba na nuna wa iyaye na hakan baza ta faru ba kuma suka amince da ni duk da a wurin mutane sai dai ka yi Allah shi ne babbar shaidar ka. Sai kuma ƙalubale na gaba shi ne, kasancewa ta mace.

Kasan akwai ƙalubale na ayyuka irin wannan na kawo wa al’umma cigaba sabo da baka san wa zaka haɗu da shi ba da matsalolin da ɗan adam yake fuskanta musamman da ya fito waje kuma musamman ‘ya mace kasan akwai ƙalubale sai dai Allah ya iya mana ta hanyar haƙuri da addu’a. Wani ƙalubale kuma shi ne kai da ka ke so kawar da kan jama’a ka talafa musu ta hanyar ilimantar da su bunƙasa kasuwancin su a zamanance na su karɓi fasarahar sadarwa a ƙudirin mu na shiga ƙananan hukumomi 44 na Kano, kasan babban ƙalubale ne ta fuskar kuɗi da kuma yadda mutane za su karɓi muradin ka har ka tallafa musu.

Me ki ke kallo a matsayin nasara?

Kai! Akwai nasara mai tarin yawa tun daga kan ko da ‘pure water’ ka ke so za ka siya da kanka ba sai ka jira wani ya baka ba. Wannan ina kallon shi a matsayin nasara ta yadda za ka dogara da kanka da tallafa wa iyayenka ko ‘yan’uwan abokan arziƙi ko badan sun rasa ba, wannan ma nasara ce a matsayi na ta ‘ya mace. Ga uwa uba haɗuwa da jama’a da suka zama abokan neman arziki wanda wani in badan wannan dalili ba ko da kuɗi baka isa ka gan shi ba. Nasara ce hakan, sannan kuma vangaren taron mu na bunƙasa sana’oinmu wanda ya haɗa ‘yan kasuwa maza da mata da yake karvuwa tun daga 2020 inda mutane 87 suka halarta. 

Haka 2021 mutane 100, 2022 mutane 300 da ‘yan kasuwa 40 suka halarta, sai kuma na bana 2023 kamfanoni na mata da maza 101 mutane sama da 600 suka halarta da sauransu. Nasara ce shi ma. Sai kuma tallafi da na samu daga ‘entrepreneurship network’ na kuɗi a taron da aka yi a Abuja, sai kuma taimakon kuɗi na NITDA ga kuma horar da matasa harkar kasuwanci ta fasahar sadarwa sama da 5000 da na horar shi ma nasara ce. Sai kuma kallo da ake min musamman ‘yan’uwana mata a matsayin wacce ke warware musu matsaloli na zamani, wato na zama wata mafita ga al’umma musamman mata. Kuma ga taruruka na ƙarin ilimi ciki harda kamfanin Facebook da suka gayyace ni taro a Legas kuma za ka ga duk turawa ne yawancin su, na karɓi lambar yabo daga mahimman wurare kamar sau biyar a rayuwata.

A kusan ƙarshe menene burinki a rayuwa?

Ina son in kafa katafaran kamfanin sadarwa wanda zai shahara A Najeriya da ma duniya bakiɗaya da kuma babar makaranta ta fasahar sadarwa da sauransu dan amfanar da al’ummar mu. Ina da burin samar da manhaja ta Hausa da dai sauran al’amura da za su kawo wa al’umma cigaba a rayuwar su. Don haka nake kira ga hukumomi da su tashi su agaza wa masu son taimakon al’umma a ko ina.

Mata kuma su dage su koyi abubuwa da duk suke so kada su ce ba za su iya ba kuma duk abin da za ki yi, ki nemi ilimin yin sa ko fasahar sadarwa ne ko ɗinki ne da sauransu, amma dai ki zama mai kame kai ta hanyar kula da addini da al’adadun mu masu kyau haka su ma matasa maza nake so su zama a rayuwar su.

Me ki ka fi so a rayuwarki?

Karance-karance da bincike da kuma zama da ƙawaye na Ina zaulayar su muna dariya muna raha muna tattauna abin da zai amfane mu duniya da lahira. Duk da ka san yawancinmu mata muna son zuwa biki, to ni ma Ina son zuwa biki da taruruka wanda za a samu ilimi mai amfani ciki.

Ya ya batun iyali ko aure ?

Maganar aure saura ƙiris da ikon Allah.

Me ki ke so ki faɗa ban tambaye ki ba?

Mutum ya yi amfani da lafiya kafin rashin lafiya, ya amfanar da rayuwarsa kafin mutuwa, ya yi amfani da ƙuruciyarsa kafin tsufa, ya yi amfani da wadatarsa kafin talaucin sa da dai sauran su. A taƙaice dai kada ayi wasa da lokaci yana da muhimmanci.

Mun gode.

Ni ma na gode.