Marubuta na taka muhimiyyar rawa a zamantakewar aure – Binta Umar Abbale

“Marubuta na fuskantar ƙalubalen satar fasaha”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Marubuta mutane ne masu martaba da kwarjini, waɗanda Allah Ya yi wa bai wa ta abubuwa daban-daban da suke amfanar da jama’a. Binta Umar Abbale na daga cikin irin marubutan da jama’a da dama ke ƙaruwa da ita. Bayan kasancewarta marubuciya, ƴar kasuwa, tana kuma bada shawarwari ga mata ta yadda za su gyara kansu da zamantakewar aurensu. Binta Abbale wacce ita ce shugabar ƙungiyar marubuta ta Manazarta Writers Association ta rubuta littattafai 19 da suka ƙunshi labarai masu ɗauke da darussa na faɗakarwa da nishaɗantarwa. A ganawarta da wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, marubuciyar ta bayyana masa abin da yake ci mata tuwo a ƙwarya game da masu satar fasaha littattafan marubuta.

MANHAJA: Ko za ki gabatar mana da kanki?

BINTA ABBALE: To, Alhamdulillahi. Da farko dai sunana Binta Umar Abbale. Ni marubuciya ce, ƴar kasuwa, kuma mai ba da shawarwari ga cigaban zamantakewar aure, musamman abin da ya shafi rayuwar mata a gidajen aure. Ina da aure da yara.

Menene taƙaitaccen tarihin rayuwarki?

A taƙaice dai, ni haifafiyar Jihar Kano ce. An haife ni a Unguwar Aisami da ke Gwauron Dutse a Ƙaramar Hukumar Gwale, kuma a nan na yi dukkan rayuwata. Na yi karatun Muhammadiya a makarantar Malam Danladi ta Ta’alimul-Ƙur’an da ke Gidan Makaranta. Sannan na yi karatun boko a makarantar Sheikh Kamalu ta Darul Ma’arif. Na kammala makarantar firamare har da sakandire duk a cikin makarantar, inda na samu nasarar kammalawa. Daga bisani kuma na yi aure, inda yanzu haka ina da yara huɗu, biyu maza biyu mata.

Waɗanne abubuwa ne na darasin rayuwa za ki iya cewa sun yi tasiri a rayuwarki, lokacin tasowarki?

Yadda iyayenmu suke ɗawainiya da mu babu gajiyawa. Da kuma irin yadda duk ƙarfinsu ya ƙare a kan mu wajen sauke nauyin da Allah Ya ɗora musu har muka kai munzalin aure, mu ma muka haifi namu. Wannan ne ya sa na fara ɗaukar darasin rayuwa, domin tun daga samun ciki zuwa raino da tarbiyya, ƙalubale ne kuma darasi ne gare mu. Lokacin duniya tana kwance, iyayenmu sun yi mana gata, a yanzu muna roƙon Ubangiji Ya sa mu kwatanta hakan a kan yaranmu.

Za ki iya tunawa da labarin da ki ka fara rubutawa? Kuma akan wanne jigo ki ka yi labarin?

Littafin farko da na fara rubutawa shi ne, ‘Nana Khadija’, shekaru takwas da suka gabata. Labarin littafin ya ƙunshi makirci ne da manaƙisa da kuma zamba cikin aminci, kan yadda wasu mata ke kaucewa koyarwar addini suna bin bokaye da malaman tsibbu, akan namiji ko kishiya. Daga ƙarshe kuma rayuwarsu ta shiga garari ba tare da sun cimma burinsu ba. To, akan wannan jigon na rubuta labarin.

Menene ya fara jan hankalinki ki ka fara tunanin zama marubuciya?

Na kasance ma’abociyar karance-karance ce da nazari. Da kuma son zaman kaɗaici. A rana tsaka Allah Ya nufe ni da fara rubutu. Kuma Ya shiga cikin lamarin, na fara a sa’a jama’a suka karɓi rubutun nawa suna yaba min da kyawawan addu’oi tare da fatan alheri.

Waye ya fara taimaka miki wajen sanin ƙa’idojin rubutu da yadda ake gina labari?

Lokacin da na fara rubutu babu wanda ya taimaka min, na sha gwagwarmaya sosai gaskiya! Saboda rubutun kawai nake yi babu ƙa’ida, sai da tafiya ta yi nisa tukkuna Allah Ya haɗa ni da wata marubuciya Zainab Shaɗɗi, sai ta kai ni wata ‘ƙungiya mai suna Zamani Writers Association. To, Alhamdullahi a ƙungiyar nan na ƙara gogewa da wasu abubuwa ta fannin sanin ƙa’idojin rubutu.

Kawo yanzu kin kai shekara nawa kina rubutu, kuma littattafai nawa ki ka rubuta?

Na yi shekara takwas ina rubutu. Kuma yanzu haka na rubuta littattafai 19. A cikinsu akwai ‘Nana Khadija’, ‘Yaro Da Kuɗi’, ‘Gimbiya Balaraba’, ‘Mashahuri’, ‘Tsantsar Butulci’, ‘Babban Yaro’, ‘Ni da Yaya Sadam’, ‘Ruwan Dare’, ‘Sadauki Omar’, ‘Yar Bangar Siyasa’, ‘Ƙwarya Ta Bi Ƙwarya, ‘Da Wata A Ƙasa’, ‘Madadi’, ‘Ga Irinta Nan’, ‘Jikar Mai Koko’, ‘Matsalarmu A Yau’, ‘Goje’, ‘Majanuni’, sai kuma ‘Ya Za A Yi?’.

Waɗanda suka fi shahara a cikinsu sun haɗa da ‘Sadauki Omar’, ‘Yar Bangar Siyasa’, da ‘Babban Yaro’. Waɗannan littattafan har yanzu sabbi ne a wajen wasu, domin kullum cikin nemansu ake yi.

A kan wanne jigo ki ka fi son gina labarin ki a kai?

Ina gina labarina ne akan abin da na san lallai yana faruwa, kuma kowanne ‘ɓangare ina taɓawa, saboda ko sunayen da nake amfani da su irin na gargajiya ne, wato asalin sunayenmu na Hausawa. Ina gina duk labaraina akan zamantakewar aure da tarbiyyar yaranmu, ƙalubalen rayuwa da sauransu.

Ta yaya ki ke sake labarinki, kina buɗe group ne a WhatsApp, ko pdf ki ke sayarwa ko kuma a manhaja?

Ina buɗe zaure ne a manhajar WhatsApp a duk lokacin da na fara sabon littafi, sai in yi ta tallansa a zauruka daban-daban har masoya su shiga. Idan na ba su shafukan kyauta sai na faɗi kuɗin cikakken littafin ga masu buƙata, don su saya a pdf su biya, su karanta gabaɗaya.

Kina yin rubutu don sha’awa ne ko don neman kuɗi?

Da farko dai sha’awa ce ta sa na fara rubutu, amma duk da haka littattafan da nake yi na kuɗi ne, ba kasafai nake littafin kyauta ba. Littattafai biyu ne kawai na yi kyautarsu ga masoya, a ciki akwai ‘Ruwan Dare’, da ‘Jikar Mai Koko’. Waɗannan su ne littattafan da na yi kyauta amma duk sauran na kuɗi ne.

Wanne tsarin kasuwancin littafin ne ya fi kawo miki riba?

E, to. Kowanne tsari ana samun alheri a cikinsa. Ina ɗora littattafai na a manhajojin sayar da littattafai daban – daban, amma a gaskiya na fi samun alheri idan na gama littafin na haɗa shi zuwa kammalallen littafi, wato document. Masu karatu sun fi samun riba saboda wasu basa buƙatar karanta labari guntu-guntu, sun fi so idan an kammala gabaɗaya sai su karanta.

Sannan ina ɗora littafina a manhajar Arewa Books. Sai dai hakan bai hana wasu da ke bayan fage ɗorawa a manhajarsu ba, wannan ƙalubalen muke ta fuskanta daga masu ɓata mana kasuwanci. Sannan kuma marubuta muna fuskantar ƙalubale sosai ta ɓangaren masu satar fasaha, ko canjin suna. Mutum zai rubuta littafi da sunansa, amma sai a samu wasu su goge sunan su mayar da nasu. Akwai kuma masu ɗaukar littafin mutum ba tare da neman izini ba su ɗora a YouTube ɗin su ko kuma su mayar da shi labarin fim ba da sanin marubucin malabarin ba.

Kawo yanzu wanne littafinki ne ya fi samun karvuwa da kawo miki kuɗi?

Gaskiya ba zan iya tantancewa ba. Alhamdullahi, sai dai na godewa Allah, domin ni gaskiya duk littafin da na yi yana samun karɓuwa a wurin jama’a. Kuma ina samun alheri har na yi wa wasu ma alheri daga cikin abinda na samu.

Ta yaya ki ke sanin jigon da ya kamata ki yi rubutu a kai?

Ina nazari ne domin hangen abinda ya cancanta na yi rubutu akai wanda na san lallai idan na yi saƙona zai isa, kuma za a amfana da shi.

Kina da YouTube Channel ne da ki ke sa littattafanki, ko sayarwa ki ke yi wasu su fitar a nasu channel din?

Ba ni da YouTube sai dai ina sayarwa ga waɗanda suke harkar, suna ɗorawa a taskar su.

Wanne lokaci ne ki ka fi jin daɗin yin rubutu?

Talatainin dare nake bi ina rubutu, ko kuma da asuba bayan na yi sallah. Domin idan ina rubutu bana son motsin komai, na kan kulle kaina a ɗaki cikin duhu a lokacin nake samun nutsuwar yin rubutu.

Ba ni labarin ƙungiyarki ta Manazarta Writers Association, me ya zaburar da ke ki ka ga ya dace ki kafata?

Na buɗe ƙungiyar Manazarta ne sakamakon wani abu da aka yi mini wanda ya sosa mini rai. Hakan ya zaburar da ni gurin ganin na himmatu da buɗe tawa ƙungiyar ta ƙashin kaina. Cikin ikon Allah ina buɗewa ta samu karɓuwa, marubuta suka dinga shiga. Yanzu haka mun kai mu 40 a ƙungiyar kuma muna tafiyar da rubutunmu cikin tsari, akwai haɗin kai a tsakaninmu sosai.

Wanne tasiri ƙungiyoyin marubuta irin naki suke takawa wajen tsaftace da inganta rubutun adabin Hausa?

To, kamar mu a ƙungiyar mu ta Manazarta muna ƙoƙarin ganin mun daidaita tunanin mambobinmu, domin ganin sun yi rubutu mai ma’ana wanda zai wa’azantar ya kuma nishaɗantar da jama’a. Alhamdullahi, kwalliya tana biyan kuɗin sabulu. Muna samun cigaba sosai ta fannin rubutunmu da kuma kyawawan addu’oi daga dubban jama’a.

Yaya ki ke fuskantar ƙalubale wajen tafiyar da ƙungiyarki, kuma wanne goyon baya ki ke samu daga mambobin ƙungiyar?

Babu wani ƙalubale sosai da zan ce ana samu a ƙungiyar mu, saboda akwai fahimtar juna a tsakaninmu. Idan na kafa doka suna ƙoƙarin ganin sun yi amfani da ita. Sai dai dole a wasu lokutan a samu saɓani, amma kuma ba ya nisa ake daidaitawa. Bayan haka kuwa ba ni da matsala da jama’ata. Muna girmama junanmu kuma muna taimakon kanmu ta hanyoyi da yawa.

A ina ki ka samu laƙabin Garkuwar Mata?

Na samu laƙabin Garkuwar Mata ne sakamakon sana’ata. Ina sayar da abubuwan da suka danganci ‘ya’ya mata. Sannan kuma ina wani zauren WhatsApp na mussaman da na buɗe don mata, da na sa wa suna Matan Albarka. Muna tattaunawa da ba da shawarwari a tsakaninmu game da matsalolin gidan aure da sauran rayuwa. Jama’a na yawan kawo min matsalolin da suka dame su. To, wannan dalilin ya sa na yi tunanin buɗe ɗin bisa amana, duk wacce take da damuwa za a bata shawarwari har ta samu mafita. Sannan kuma duk wacce ta ji wani abin ƙaruwa daga waje za ta zo ta faɗa mana, domin kowa ya amfana. Muna taimakon junanmu sosai da shawarwari da kuma addu’o’i, domin neman mafita a gurin Allah.

Wacce rawa mata marubuta ke takawa wajen kyautata zaman aure da tarbiyyar matasa?

Marubuta mata suna taka muhimiyyar rawa wajen daidaita zamantakewar aure da tarbiyyar yara. Rubutu yana da saurin isar da saqo mutuƙar mai karantawa zai yi amfani da abinda marubuci ya rubuta, domin isar da saƙo. Da yawa marubuta suna ƙoƙarin ganin sun gina labari akan abinda zai amfani al’umma, ya kuma taimaka gurin tarbiyyar yaranmu.

Bayan harkar rubutun adabi, waɗanne harkoki ki ke yi na inganta rayuwarki da iyalinki?

Ina kasuwanci kamar yadda na yi bayani da farko. Kuma ina ƙoƙarin ganin na kula da yarana ta fannoni da yawa. Harkokina na yau da gobe ba sa hana ni kula da gida da kuma kula da haƙƙin yarana.

Wanne buri ki ke da shi nan gaba na ganin harkar rubutun adabi ta kai nan da wasu shekaru?

Ina da burin ganin harshen Hausa ya bunƙasa a duniya ya zarce kowanne harshe. Shi ya sa nake girmama ‘yan uwana marubuta, domin muna ba da gudumawa sosai gurin bunƙasa adabi, don isar da saƙo da abinda zai amfani al’umma.

Wacce karin magana ce ke tasiri a rayuwarki?

Idan rana ta fito tafin hannu ba ya kare ta.

Na gode.

Ni ma ina godiya.