Birtaniya ta burge Nijeriya

Ƙasar Birtaniya wacce ita ce ta raini Nijeriya har zuwa lokacin samun ’yancin kai a shekara ta 1960 ta faranta ma duk wani ɗan ƙasa na ƙwarai rai bisa ayyana ƙungiyar ‘yan ta’adda ta IPOB a matsayin ‘yan ta’adda.

Kamar yadda tashar radiyon BBC Hausa ta yi hira da mai magana da umurnin shugaban ƙasa Malam Garba Shehu ya yi ƙarin haske da nuna farin cikin gwamnatin ƙasarmu cewa ƙasar Birtaniya ta yi abin ƙwarai ganin yadda IPOB ta zamo annoba.

Muna fatan ƙasashe kamar Amurka ita ma ta biyo bayan ƙasar Birtaniya wajen haramta waccen ƙungiya ta ‘yan ina da kisa IPOB wanda hakan zai ƙara azama ga Hwamnatin Nijeriya ta ƙara zage dantse a kakkaɓe su domin al’umma ta zauna lafiya.

Daga MUKHTAR IBRAHIM SAULAWA. 07066434519 – 08080140820.