Ƙasashen BRICS sun yi kira a haɗa kai don tinkarar sauyin yanayi

Daga CMG HAUSA

Kwanan nan ne aka gudanar da babban taron ƙasashen BRICS kan tinkarar sauyin yanayi ta kafar bidiyo, inda aka yi kiran a hada kai don tinkarar matsalar sauyin yanayi, da tattaunawa kan gaggauta rage fitar da iskar dake gurbata muhalli, da lalubo hanyar samun farfaɗowa mai ɗorewa da daidaito da nuna haƙuri.

Ministan kula da muhallin halittun ƙasar Sin, Huang Runqiu ya gabatar da jawabin dake cewa, ta hanyar shirya babban taron ƙasashen BRICS kan tinkarar sauyin yanayi, ƙasar Sin na fatan yin ƙoƙari tare da kasashen BRICS, don tabbatar da aiwatar da ra’ayin kasancewar bangrori daban-daban a duniya, gami da yarjejeniyar tinkarar sauyin yanayi ta Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma yarjejeniyar Paris, a wani ƙoƙari na kafa tsarin kula da yanayin duniya mai adalci da samar da moriya ga kowa, da kiyaye duniyarmu yadda ya kamata. Minista Huang ya kuma bayyana manufofi gami da matakan da ƙasarsa take ɗauka a fannin sauyin yanayi.

A nasa ɓangaren, wakilin ƙasar Sin na musamman mai kula da harkokin tinkarar sauyin yanayi, Xie Zhenhua ya nuna cewa, ƙasarsa tana goyon-bayan ƙasar Masar wajen gudanar da taro karo na 27 na ƙasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar tinkarar sauyin yanayi ta MƊD, wato COP27 a taƙaice, don yin ƙoƙari tare da ɓangarori daban-daban, wajen gudanar da taron cikin nasara.

Mai Fassara: Murtala Zhang