Daga CMG HAUSA
Ranar 13 ga wata, aka rufe taron koli na musamman tsakanin ƙasar Amurka da ƙasashe mambobin ƙungiyar ASEAN a birnin Washington, babban birnin ƙasar, wanda aka dakatar da kira a baya. Sai dai babu wani abu takamaimai cikin sanarwar haɗin gwiwa da aka bayar bayan rufe taron.
Manazarta sun yi nuni da cewa, lamarin bai wuce zaton mutane ba, wato Amurka ta yi shelar ƙara yin abota da ƙasashen Asiya, amma haƙiƙa dai tana yunƙurin haɗa hannu ne da waɗanda ke adawa da ƙasar Sin.
Kafofin yada labaru na ƙasashen duniya sun lura da cewa, Amurka ta yi alƙawarin zuba wa ƙungiyar ASEAN dalar Amurka miliyan 150 a wannan karo. Amma akwai ƙasashe mambobi guda 10 cikin ƙungiyar ta ASEAN, don haka kuɗin da ko wace ƙasa za ta samu ba shi da yawa sam.
Haka kuma a ‘yan kwanakin baya, majalisar wakilan Amurka ta zartas da shirin dokar tallafawa ƙasar Ukraine da ke shafar dalar Amurka biliyan 40. Ƙasashe mambobin ƙungiyar ta ASEAN sun ƙara fahimtar matsayinsu a wajen Amurka. Amurka ba za ta iya lallashinsu ba.
Har kullum ƙungiyar ta ASEAN na tsayawa tsayin daka kan kiyaye ‘yancin kansu da kuma tafiyar da harkokinsu da kansu. Sun san nufin Amurka na shirya wannan taron koli sosai. Ferdinand Romualdez Marcos, shugaba mai ci na ƙasar Philippines ya bayyana a fili cewa, ƙasarsa ba za ta kulla kawance da manyan ƙasashe ba, za ta tsara manufofinta na jakadanci da kanta.
Wannan shi ne dalili da ya sa tsarin tattalin arziki na tekun Indiya, da tekun Pasifik da Asiya da Amurka ta gabatar, bai samu amincewa tsakanin ƙasashe mambobin kungiyar ASEAN ba. Har ma kafofin yada labaru na Amurka sun ce, babu wani abu takamaimai da tsarin ya kunsa, inda suka bayyana shi a matsayinsa wata manufa maras amfani.
Mai fassara: Tasallah Yuan
