Ya kamata Sin da Amurka su ƙara haɗin gwiwa a fannin aikin noma

Daga CMG HAUSA

An gudanar da taron tattauna bunkasa aikin noma da yankunan karkara tsakanin ƙasashen Sin da Amurka ta yanar gizo a baya bayan nan, wanda kwalejin ilmin bunkasa ƙasa da ƙasa da aikin noma ta duniya, ta jami’ar ilmin aikin noma ta ƙasar Sin ta ɗauki baƙuncinsa.

Mahalartar taron na ganin cewa, ya kamata Sin da Amurka su ƙara hadin gwiwa a fannin aikin noma, suna cewa, hakan zai amfanawa ƙasashen biyu, har ma da samar da gudummawa ga tabbatar da wadatar hatsi a duniya.

Bisa ƙididdigar da aka yi, yawan kuɗin cinikin aikin noma da aka samu tsakanin Sin da Amurka a shekarar 2021 ya kai dalar Amurka biliyan 46.4, wanda ya kai matsayin koli a tarihi. Tsohuwar gwamnar jihar Iowa ta ƙasar Amurka, Patty Judge ta bayyana cewa, ƙara haɗin gwiwar cinikayyar aikin noma tsakanin Amurka da Sin yana da muhimmanci sosai kan aikin noma, kana ƙasashen biyu za su samu moriyar juna. Ta ce a halin yanzu, ya kamata ƙasashen biyu su nemi hanyoyi da damar yin mu’amala da juna, kana mu’amalar dake tsakanin ƙwararru na ƙasashen 2 masu nazarin aikin noma, za ta taimakawa raya dangantakar dake tsakaninsu.

Shugaban kwalejin nazarin tattalin arziki da manufofi a fannin abinci na duniya ta jami’ar ilmin aikin noma ta ƙasar Sin, Fan Shenggen ya bayyana a gun taron cewa, farashin abinci a duniya yana ƙaruwa, yana mai cewa hakan ya kawo barazanar matsalar yunwa ga jama’ar Afirka da kudancin Asiya. Ya ce kiyaye farashin abinci a duniya muhimmin nauyi ne da ya kamata Sin da Amurka su sauke don samarwa kowa abinci mai inganci kuma mai gina jiki, kana aiki ne da ya shafi kowane bangare, don haka ya kamata dukkan ƙasashen duniya su yi kokarin haɗa hannu wajen daidaita matsalar.

Mai fassara: Zainab