Bisa aiki tuƙuru Sin ta samu karɓuwa a ƙasashen Afirka

Daga CMG HAUSA

A baya bayan nan, tawagar masana ta ƙasar Kenya, mai lakabin “Cibiyar raya tattalin arzikin yankin gabashin Afirka”, ta fitar da rahoto, na sakamakon wani bincike game da tasirin haɗin gwiwar Sin da ƙasashen Afirka.

Rahoton ya yi nuni da yadda ƙasashen Afirka ke jinjinawa ingancin ababen more rayuwa da Sin ke ginawa a nahiyar, da saurin aiwatar da manufofi, da kammala ayyuka a kan lokaci.

Dalilai na zahiri sun tabbatar da cewa, Sin na aiwatar da matakai masu nagarta da inganci, ta kuma samar da moriya mai yawa, da damammaki na ingiza ci gaban Afirka, matakin da ya samar mata da amincewa da yabo.

Mai fassarawa: Saminu Alhassan daga CMG Hausa