Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce biyan kudin fansa ga ‘yan bindiga na kara musu karfin gwiwa tare da ba su damar sayen manyan makamai.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Channel, inda ya sake jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta tattauna da ‘yan bindiga domin biyan fansa ba.
Ya ce, “Matsayina tun daga farko shi ne ba za mu yi sulhu da ‘yan bindiga ba, kuma har yanzu ina kan wannan matsayar.”
Lawal ya ce satar mutane domin neman kudin fansa ta zama tamkar sana’a ga wasu ‘yan bindiga, inda kudaden da suke karba daga iyalan wadanda suka sace suke amfani da su wajen sayen makamai.
Ya ce, “Duk kudin da aka ba su, suna amfani da shi ne wajen sayen manyan makaman da suke amfani da su. Idan ba su samu kudin ba, ta yaya za su samu wadannan makaman?”
Gwamnan ya kuma bayyana cewa wasu daga cikin ‘yan uwansa biyu sun taba shiga hannun masu garkuwa da mutane, inda aka bukaci a biya Naira miliyan 300 kan kowane mutum.
Ya ce duk da bukatar masu garkuwar, ya ki biyan kudin, yana mai cewa ba zai ba mai laifi kudi domin ya kara karfin aikata laifuka ba.
“Ba zan ba da kudina ga mai laifi domin in karfafa shi ya kara aikata irin wannan laifi ba,” in ji Lawal.
Da yake magana kan tattaunawar da gwamnatocin baya suka yi da ‘yan bindiga, Lawal ya ce irin wannan mataki bai haifar da sakamako mai kyau ba saboda, a cewarsa, ‘yan bindigar ba su da tsari ko shugabanci guda.
Ya ce idan gwamnati ta tattauna da wata kungiyar ‘yan bindiga, wata kungiyar na iya ganin an raina ta ko ba a ba ta muhimmanci ba, wanda hakan ke kara rikita lamarin.
Lawal ya ce rashin samun shugabanci guda daga bangaren ‘yan bindigar na sa tattaunawa da su ta kasance mai wahalar cimma matsaya.
