Bobrisky ya shaƙi iskan ‘yanci

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Fitaccen ɗan daudu Idris Okuneye, wanda aka fi sani da Bobrisky ya fito daga gidan kaso bayan shafe tsayin watanni a gidan gyaran hali.

Kamar yadda jaridar Blueprint ta ruwaito a ranar 5 ga watan Afrilun 2024, hukukar EFCC ta cika hannu da fitaccen ɗan daudu, namiji mai shiga irin ta mata, Bobrisky, wanda ake wa inkiya da Mummy of Lagos, kan zarginsa da ake yi da cin zarafin takardun Naira.

Yayin da a ranar 15 ga watan na Afrilun aka tasa ƙetarsa zuwa gidan gyaran hali, bayan wata kotu ta kama shi da laifin na cin mutuncin takardar Naira.

A wani faifan bidiyo da aka wallafa a ranar Litinin ɗin da ta gabata, ya nuna Idris Okuneye Olarenwaju, wanda aka fi sani da Bobrisky na murna tare da wasu abokanenshi,  jim kaɗan bayan fitowarsa daga gidan yari.

Bonbrisky ya yi godiya ga ‘yan uwa da abokai, waɗanda ya ce, sun tsaya masa a lokacin da kotu ta tura shi gidan gyaran hali.

Wasu daga abokanen nasa sun wallafa saƙon taya murna na fitowar ɗan uwan nasu, inda suke cewa, “Mun fito daga gidan kaso, muna taya ka murna Bobrisky.”

By ukarofi