Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Hukumar Kula Da Hidimar ƙasa ta NYSC ta yi gargaɗin cewa waɗanda suka kammala karatu a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ba tare da shaidar zuwa aikin horo ‘IT’ na shekara guda ba, ba za a ba su damar shiga NYSC ba.
Kodinetan NYSC a jihar Legas, Yetunde Baderinwa, ta bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ranar Asabar a Legas.
Baderinwa ta ce, hukumar ta NYSC ta fitar da wata sanarwa a kan hakan.
Baderinwa ta ce, “An lura a ’yan kwanakin nan cewa wasu ɗaliban da suka kammala karatu a polytechnics ba sa kiyaye wajabcin zuwa IT na shekara ɗaya kafin a ba su damar shiga HND.
“Tsarin IT na shekara guda shi ne abin da ake buƙata don HND. Dole ne su yi aikin IT na shekara guda tare da shaidar kammala karatunsu kafin su tafi HND, kuma dole ne hukumomi su tabbatar da hakan kafin su shigar da su HND.
“Wannan umarni zai fara aiki ne daga sansani na gaba, kuma ba za mu yi rajistar duk wani ɗalibi da bai gudanar da IT ba.”
Ta ce, matakin zai inganta tsarin ilimin Nijeriya.
