Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
’Yan ta’addar Boko Haram sun kai hari kan al’ummar jihar Borno tare da kashe mutane biyu tare da ƙona wani coci.
Ana kiran ƙauyen da suna Bamzir da ke ƙarƙashin gundumar Wuntaku a ƙaramar hukumar Chibok.
A cikin wata sanarwa da tawagar manema labarai ta shugaban ƙaramar hukumar Chibok Mustapha Madu ta fitar ta ce ‘yan ta’addan sun kai hari ne da misalin ƙarfe 2:10 na safiyar Lahadi tare da ƙona gidaje da dama wanda ya yi sanadin mutuwar wasu ‘yan uwa guda biyu, mai suna Josiah Pogu Pudza, ɗalibin ajin SS 2 na sakandare, da Enoch Pogu Pudza yayin da ɗaya Esther Yohanna ta samu rauni da harsashi.
Sanarwar ta ƙara da cewa, ‘yan ta’addan sun kwashe kayan abinci da dabbobi, tare da ƙona ɗakin taro na cocin EYN LCC, da gidaje da shaguna da dama.
An binne mutanen biyu da sanyin safiya. Shugaban ƙaramar hukumar Mustapha Madu ya halarci taron.
Mustapha ya jajantawa iyalan waɗanda suka rasu, ya kuma duba duk wasu gidajen da suka ƙone, shaguna, da ɗakin taro na coci.
Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne na Lakurawa suka kashe mutane da dama a jihar Kebbi da ke Arewa maso Yamma.
Sun kashe ma’aikatan sadarwa guda biyu da ɗan asalin ƙauyen Gumki da ke ƙaramar hukumar Arewa a jihar Kebbi.
‘Yan ta’addan sun mamaye al’ummar yankin inda suka aikata wannan mummunan aiki a lokacin da waɗanda abin ya shafa ke sanya abin rufe fuska a yankin.