Borno za ta daƙile kwararowar yara marasa ‘yan rakiya da ke shiga jihar

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Jihar Borno ta jaddada ƙudirinta na magance kwararowar yaran da ba su da ‘yan rakiya a jihar.

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Tsaro na Cikin Gida, Farfesa Usman Tar, ya bayyana haka bayan taron Majalisar Tsaron Jihar a ranar Litinin.

Babagana Umara Zulum, gwamnan jihar Borno ne ya jagoranci taron wanda ya gudana a zauren majalisar na gidan gwamnati.

Kwamishinan ya ce, “Majalisar ta yi taro a yau Litinin 5 ga watan Agusta, 2024, domin duba halin tsaro a jihar. Bayan yin nazari sosai kan duk abin da ya faru daga ranar 1 zuwa 5 ga watan Agusta, majalisar ta cimma matsaya.”

Ya ƙara da cewa, daga cikin ƙudurorin da aka cimma, kwamitin tsaro ya amince da cewa, za a riƙa sa ido da kuma kula da jigilar yaran da ba sa rakiya zuwa Maiduguri daga yanzu. Ya ce, yaran da aka gano suna da kulawar iyaye ne kawai za a bar su su shiga babban birnin jihar.

Kwamishinan ya kuma ƙara da cewa gwamnatin jihar Borno ta sha alwashin ci gaba da baiwa jami’an tsaro goyon baya wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na tabbatar da doka da oda a Borno.

Ya kuma ce wani ɓangare na ƙudurin majalisar shi ne tabbatar da cewa an gaggauta gurfanar da waɗanda aka kama tare da gurfanar da su gaban kuliya.

Hakazalika kwamishinan ya bayyana cewa za a bi shari’o’in ƙananan yara yadda ya kamata, kuma an bai wa ma’aikatar shari’a umarnin samar da tsarin shari’ar ƙananan yara nan take.

Ya buƙaci jama’a da su tallafa wa jami’an tsaro da bayanan sirri domin su taimaka wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Borno.

By ukarofi