A ƙara haƙuri, bayan wuya sai daɗi – Tinubu ya roƙi ‘yan Nijeriya 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya roƙi ‘yan Nijeriya da su ƙara yin haƙuri da gwamnatinsa, inda ya tabbatar da cewa ƙasar nan na dab da shiga sabon shafi.

Tinubu ya yi riƙon ne a ranar Laraba, inda ya tabbatar da cewa yasan ‘yan Nijeriya na cikin matsi sakamakon janye tallafin man.

“‘yan uwa ‘yan Nijeriya, wannan lokaci zai zama mai wuya gare mu, babu makawa muna cikin yanayi na wahala amma ina buƙatar mu yi haƙuri da wannan yanayi na wucin gadi. Dukkan tsare tsarenmu masu kyau suna aiki. Mafi muhimmanci shi ne nasan za su yi aiki.”

Shugaban ƙasar ya tabbatar da cewa matakan da gwamnatinsa take ɗauka zai fitar da ƙasar nan daga matsin tattalin arziki, inda ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su miƙa yardarsu ga gwamnatinsa.

“Ina roƙon ku, ku miƙa yardarku kan ƙoƙarinmu na sauke nauyi kuma mun damu da walwalar mu.”

Tinubu ya kuma jadadda ƙudurinsa na bayar damar samun ilimi ga ‘yan Nijeriya ta hanyar fito da tsarin bashin karatu ga ɗalibai.

By ukarofi