An zargi Dangote da amfani da arzikin Nijeriya don zama mafi kuɗi a Afirka

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Lauyan mai fafutukar kare haƙƙin ɗan adam, Deji Adeyanju ya zargi hamshaƙin ɗan kasuwa, Aliko Dangote da yin amfani da kuɗin Nijeriya wajen zama mutumin da ya fi kowa arziki a Afirka duk shekara.

Lauyan tsarin mulki ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo na The Honest Bunch.

A cewarsa, Dangote ya karya ‘yan kasuwa da dama a Nijeriya saboda ya ɗare sama.

Ya ce; “Aliko Dangote mutum ne da ya kamata ya ji kunya, yana amfani da kuɗin Nijeriya wajen zama mutumin da ya fi kowa kuɗi a Afirka duk shekara. Ya kashe kasuwanni da yawa don haka ban san dalilin da ya sa yake kuka ba.

“Dangote ba ya son gasa. Abin da ya ke yi shi ne, kafin kowace gwamnati ta hau mulki, sai ya tantance wanda zai yi nasara ya ba su gudunmawar kuɗi.

“Kuma idan suka karɓi mulki, sai ya je yin mubaya’a a gare su, abin takaici, hakan bai yi aiki da Tinubu ba, shi ya sa suke fushi da shi.

“Sun takura masa ne saboda su kansu makusantan Tinubu kawai suna saka wa gaba, kamar Dangote. Suna jin babu wani abu da Dangote zai iya yi wanda ba za su iya ba. Za su iya yin harkar mai kuma su kawo sukari.

By ukarofi