CBN ya amince da haɗakar bankin Unity da Providus

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A ranar Talata ne Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sanar da amincewa da wani muhimmin mataki don tallafawa shirin haɗewar bankin Unity da Bankin Providus Bank.

Babban bankin, a cikin wata sanarwa da muƙaddashin Daraktan Sadarwa na Kamfanin, Hakama Sidi-Ali, ya fitar, ya ce an tsara matakin ne domin ƙarfafa zaman lafiyar tsarin hada-hadar kuɗi da kuma kaucewa haɗarin da ke tattare da tsarin.

“Haɗin gwiwar ya ta’allaƙa ne kan tallafin kuɗi daga CBN. Asusun zai taimaka wajen magance jimillar ayyukan Bankin Unity ga Babban Bankin da sauran masu ruwa da tsaki,” inji sanarwar.

“Babu shakka a bayyana cewa matakin na CBN yana ƙarƙashin tanadin sashe na 42 (2) na dokar CBN, na shekarar 2007. Wannan tsari yana da matuƙar muhimmanci ga harkar kuɗi da daidaito.

“Yana da muhimmanci a nanata cewa babu wani bankin Nijeriya a halin yanzu da ke fuskantar wani mawuyacin hali kamar na bankin Heritage, wanda aka rushe kwanan nan.”

Babban bankin na CBN ya ce ya ci gaba da jajircewa wajen kare muradun masu ajiya da kuma tabbatar da tafiyar da harkokin bankin cikin sauƙi ta hanyar ɗaukar matakai da dabaru.

By ukarofi