Kotu ta amince da bai wa shugabannin ƙananan hukumomi damar wa’adin mulkin shekaru huɗu

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kotun ƙolin Nijeriya ta yanke hukunci kan dokar ’yancin cin gashin kai ga ƙananan hukumomi inda ta bai wa shugabannin ƙananan hukumomi damar samun wa’adin shekaru huɗu a ofis a faɗin ƙasar.

Wannan yana ƙunshe ne a cikin takardar Certified-True-Copy (CTC) na hukuncin da mai shari’a Mohammed Garba da wasu shida suka yanke ranar 11 ga Mayu, 2024.

Garba ya ce, wasu jihohi suna tauye ‘yancin ƙananan hukumomi a jihohinsu, ta yadda akasarin su ba za su iya yin aikin da kundin tsarin mulki ya ba su ba, ko kuma gudanar da ayyukansu na doka.

Mai shari’a ya bayyana halin da ƙaranan hukumomi ke ciki a ƙasar a matsayin “matakin rashin mutunta gwamnati zuwa wani ɓangare na gwamnati.”

Garba ya ce, ƙananan hukumomi a Nijeriya ba kamar rassan hukumomi ba ne, a tsarin mulkin ƙasa mataki na uku ne na Gwamnatin Tarayya.

A cewarsa, ‘yancin cin gashin kansu na siyasa da na kuɗi yana bisa tsarin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya na shekarar 1999 (kamar yadda aka yi wa kwaskwarima.

Mai shari’a ya ce, sashe na 2 (2) na kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanadi cewa “Nijeriya za ta zama Tarayyar da ta kunshi Jihohi da Babban Birnin Tarayya”.

Ya kuma bayyana cewa, an ƙayyade kujeru 36 a ƙasar nan, a tsarin haruffa, ta sashe na 3(1) na kundin tsarin mulkin ƙasar.

Ya ce sashe na 3 (6) na kundin tsarin mulkin ƙasar, ya tanadi cewa “za a samu ƙananan hukumomi 768 a Nijeriya” yayin da sashe na 1 (2) na kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada cewa “Ba za a gudanar da mulkin Nijeriya ba, ko wani mutum ko gungun jama’a ba za su mallaki gwamnatin Nijeriya ko wani ɓangare nata ba, sai dai bisa tanadin kundin tsarin mulkin ƙasar.”

By ukarofi