Daga MAHDI M. MUHAMMAD
A wani lamari mai ban al’ajabi a makarantar firamare ta Ford da ke Detroit, Michigan, ƙuianna Hudson ‘yar shekara 8 ta kawo bindigar mahaifinta makaranta kuma ta harbe malaminta mai shekaru 56 mai suna Jim Turner har lahira.
Rahotanni sun nuna cewa Turner ya kira Quianna a cikin ofishinsa a lokacin da ake karatun motsa jiki, bayan wasu ‘yan lokuta sai aka ji harbi sau biyu, lamarin da ya sa ɗalibai suka yi ta firgita.
Jami’an tsaron makarantar sun yi gaggawar zuwa wurin, inda suka iske Turner ya mutu, da harbin bindiga a cinyarsa da kuma ƙirjinsa.
’Yan sanda sun isa wurin ba da jimawa ba kuma suka kama Quianna.
A hannun ’yan sanda, Quianna ta bayyana cewa Turner yana shafa mata jiki da niyyar yi mata fyaɗe kuma yana barazana ga rayuwarta idan ta kai rahoton ga wani.
Tsoron kare lafiyarta, Quianna ta ɗauko bindigar mahaifinta daga ƙarƙashin katifa ta kawo ta makaranta don kare kanta.
Bidiyon sa ido na CCTV ya tabbatar da maganar Quianna, inda aka ga Turner yana yawan kiranta ofishinsa.
Ana sa ran iyayen Quianna za su fuskanci tuhuma dangane da mutuwar Turner.
Al’umma sun yi kaca-kaca a kan lamarin; wasu mazauna garin na nuna shakku kan ikirarin ƙuianna, ciki har da malama Lorraine Jacobs, wanda ya shaida abin da ya biyo baya.
“Na san Jim shekaru da yawa. Ba irin wannan mutumin ba ne,” inji ta.
Akasin haka, wasu membobin al’umma sun bayyana goyon bayansu ga ƙuianna.
“Idan yana cutar da ita, abin da ya kamata ta yi don ta kare kanta,” inji wani mai goyon bayanta.
