Har yanzu Tinubu yana biyan tallafin man fetur, inji Obasanjo

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa an dawo da tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta cire a shekarar 2023 sakamakon hauhawar farashin kayayyaki.

Idan za a iya tunawa, Shugaba Bola Tinubu a jawabinsa na farko a ranar 29 ga Mayu, 2023, ya bayyana cewa tallafin man fetur “ya ƙare.”

Wannan lamari ya haifar da tashin farashin man fetur daga kimanin N200 zuwa sama da N600 kowace lita.

A wata hira da jaridar Financial Times, Obasanjo ya caccaki yadda gwamnati ta cire tallafin.

A cewarsa, kamata ya yi gwamnati ta aiwatar da wasu matakai kafin cire tallafin.

Ya bayyana cewa tallafin ya “dawo” saboda yawan hauhawar farashin kayayyaki.

“Akwai ayyuka da yawa da ya kamata a yi. Ba wai kawai ka tashi da safe ka ce ka cire tallafin ba. Saboda hauhawar farashi, tallafin da aka cire bai tafi ba. Ya dawo,” inji Obasanjo.

Ya kuma bayyana buƙatar amincewar masu zuba jari a Nijeriya, yana mai cewa, “Dole ne ku fita daga tattalin arzikin kasuwanci zuwa tattalin arzikin canji.”

Jawabin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da zanga-zangar yunwa a Nijeriya.

By ukarofi