Idan ana batu a kan kishin ƙasa da al’ummar ƙasa, to ko shakka babu sai an cire son zuciya, wanda hakan shi zai bada damar tabbatar da samun zaman lafiya ga ƙasa, ta yadda ‘yan ƙasa za su rayu cikin aminci.
Babu wani abu da zai faru a cikin ƙasa na koma-baya a ɓangaren tsaro da za a ce hukumomin tsaro sun kasa sanin wannan abin. Ina nufin duk abinda ke faruwa a ƙasa na shige-da-fice a ko ina, to babu abinda yake ɓoyuwa ga jami’an tsaro da zai gagare su sani. Domin a kowacce hukumar tsaro akwai (interllagents), wato ƙwararru da suke binciko ko gano wani abu da aka kitsa shi a sirri, in ma don a yi ta’addanci ko akasin haka.
Magana ta gaskiya a nan ita ce, idan har jami’an tsaron Nijeriya za su tsaya tsakani da Allah suyi aiki ba tare da son zuciyarsu ko ta iyayen gidansu ba, to a cikin lokacin da ba mai yawa ba za a iya kawo ƙarshen duk wata matsala ta rashin tsaro da ake fama da ita a Nijeriya. Tarihi ya nuna yadda aka yi yaƙin Ojuku aka yi galaba a kansa, haka nan Buba Marwa da aka fi sani da (Mai Ta-tsine) a Kano, da Biafra da sauransu.
Abinda nake so na tunasar da jami’ai da dukkan hukumomin tsaro shi ne, su sani cewa ba su da wata ƙasar da ta wuce ƙasar nan tamu Nijeriya, kuma tilas ne su kare ƙasa da al’ummar ƙasa. Sun san da haka, sun kuma yarda wajibi ne a kansu aiwatar ko samar da tsaro ga al’umma da dukiyarsu, domin sun yi rantsuwa kan hakan kamar yadda yake rubuce, kuma doka a cikin kundin ƙasa.
Idan hukumomin tsaro sun kare mutuncin ƙasa da al’ummar ƙasa ba taimakon al’umma da ƙasa suka yi ba, haƙƙin da ke kansu ne na nauyin yin hakan suka sauke, idan kuma ba su sauke nauyin da ke kansu na kare ƙasa da al’ummar ƙasa ba, to sunansu maciya amanar ƙasa da al’ummar ƙasa. Babu wata ƙasa da zata baro ƙasarta da al’ummarta su zo suyi mana maganin duk wata matsala da ta same mu, kenan ya zama wajibi hukumomin tsaron Nijeriya ku san da wannan.
Muna kallon yadda ‘yan ta’adda suke yin abinda duk suka ga dama a Nijeriya, ana kashe al’umma, ana kama su ana kaiwa daji ana azabtar dasu, sannan daga baya a nemi kuɗin fansa a biya. Abin mamakin kuma hukumomin tsaro sun kasa magance wannan matsalar, matsalar da bata fi ƙarfin a murƙushe ta ba. Kuma babban abin takaicin shi ne, waɗanda suke aikata wannan ta’addanci an sansu, an san inda suke. Kai ƙarshe ma an san wace ƙabila ce suke aikata hakan, ‘yan Nijeriya ba daga wata ƙasar suka zo ba, amma an zuba musu ido kullum abin ƙaruwa yake yi.
Ta kai ta kawo tun ana satar shanu, aka dawo kashe mutane ana kwashe musu dukiya, sannan aka dawo ana satar mutane ana neman kuɗin fansa. A ƙauyuka da manyan hanyoyi za a tare matafiya a mota a kwashe a kora su daji daga baya a nemi kuɗin fansa, sannan za a ɗauki bidiyo a ɗora a shafin yanar gizo, amma duk wannan abin ba ya hana ‘yan uwan waɗanda a ka ɗauka su haɗa kuɗi sukai don a sako musu ‘yan uwansu.
Idan har jami’an tsaro a ƙasar nan suna aiki tsakani da Allah don kishin ƙasa, yaushe ɗan ta’adda zai tare mota a hanya ya kwashi mutane ya kai daji ya ɓoye ba a kama shi ba? Ko kuma ya je har gida, ko cikin gari ya ɗauki mutum ya yi garkuwa da shi ba a kama shi ba? ‘Yan ta’addar nan suna amfani da wayar hannu, suna da ababen hawa, dazukan nan da suke ɓuya suna ta’addanci a Nijeriya suke ba a Kamaru, Chadi ko Nijar ko kuma a Canada ko Algeria suke ba. Dazuka ne namu na Nijeriya, kuma babu wani dajin da hukumomin tsaro ba su san yanda yake ba.
Lokacin tsohuwar gwamnatin Buhari da ta gabata, mun ga irin yadda ya riƙa yawace-yawace a ƙasashe maƙwafta da kuma nahiyar Turai da sunan difilomasiyya, ko mu ce ƙawancen ƙasashe don haɓɓaka ci gaban ƙasarmu Nijeriya, amma daga ƙarshe me hakan ya tsinana mana banda koma-baya? Wacce ƙasa ce za ta yarda ta ƙulla wani ƙawancen hulɗar arziki da ƙasarmu Nijeriya, har ta kai ga anyi kasuwanci don mu amfana? Hakan ba zai yiwu ta cikin sauƙi haka kawai ba, domin ƙasashen duniya sun riga sun san cewa Nijeriya ƙasa ce mai cike da arziki, amma kuma zagaye take da ɓeraye da Gafiyoyi maciya amana. Don haka, ba za su yarda su zuba hannun jarinsu a Nijeriya ba.
Yau shekararmu 64 da samun ‘yancin kai a Nijeriya, mun rabu da mulkin soja a shekarar 1999, yanzu shekara 25 kenan ana mulkin farar hula (mulkin dimokraɗiyya), amma kullum ci baya muke yi ba ci gaba ba, idan kuwa har abubuwan da suke faruwa a Nijeriya yanzu ci gaba ne, to sai dai a kira hakan da ci gaban mai tonon rijiya. Tun zuwan Buhari a shekarar 2015 muka koma baya da 90% Nijeriya ta taɓarɓare, ɗan jin daɗin shi ne 10% wanda a yanzu ya sake raguwa ya koma 5%.
Amma a yau Buhari na ɗaya daga cikin tsaffin shugabannin da suka je Abuja fadar shugaban Nijeriya Tinubu dake kan mulki a yanzu, suka nuna goyon bayansu tare da yaba wa da salon mulkinsa. Da Buhari yayi abin kirki a gwamnatinsa, to na tabbata ba zai goyi bayan abinda Tinubu yake yi a yanzu ba, amma da yake salonsu ɗaya, manufar ma ɗaya ce, wato ɗanjuma ne da ɗan Jimmai, shi ya sa a yau tsohon shugaban Nijeriya Buhari yake murna da farin ciki game da yadda Tinubu yake tafiyar da mulki a Nijeriya.
Salo marar ma’ana, salo na kaico da takaici gami da sanin mece ce makomar ‘yan ƙasa? Buhari ya yi wa Nijeriya illar da sai an ɗauki shekaru kafin a iya gyara ƙasar ta dawo daidai, ba sharri ko ƙage da yarfe nake yi masa ba, wallahi ina da tarin hujjoji. Tun farkon gwamnatinsa bai zo da kyakkyawar manufa ta alkhairi ga ƙasa da al’ummar ƙasa ba, shi ya sa Allah bai ba shi nasara ba, kuma duk abinda ya faɗa a baya yaudara ce da kwaɗayin mulki. Idan ba a manta ba an gan shi ya jagoranci mutane zanga-zangar ƙin jinin gwamnati a lokacin shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, ya fito ya ƙalubalenci salon mulkin Marigayi Alh. Umar Musa ‘Yar’adua lokacin da yake shugaban ƙasa kafin Jonathan ya gaje shi. Buhari ya bayyana cewa, “Idan ‘yan Nijeriya suka sayi litar mai sama da Naira 50 an zalunce su…” da sauran maganganu da dama marasa kangado da ya riƙa yi na nuna adawa da kushe gwamnatin ‘Yar’adua da Jonathan.
Don haka, ina so ‘yan ƙasa ku sani cewa, duk abinda ke faruwa na rashin tsaro, da yunwa da ta addabi jama’ar Nijeriya, wallahi tallahi abubuwa ne da hukumomi sun san duk yadda za su yi su kawo ƙarshensu, kawai dai ba za su yi ba ne. Tabbas akwai waɗanda suke cin moriyar rashin tsaro ta hanyar siyasantar da abin suna kasuwanci tare da kwangilar kashe mu raba, da kuma gurɓatattun ‘yan siyasa da suke amfani da hakan wajen neman madafun iko, sai kuma ‘yan rashawa da cin hanci, da waɗanda suke amfani da matsalar rashin tsaro da yunwa da ke damun al’umma suna kwashe dukiyar ƙasa. To dukkanninsu waɗannan ba za su taɓa so Nijeriya ta zauna lafiya ba, kuma akwai su a cikin jami’an tsaro kowanne nau’i, akwai su a shugabannin al’umma ‘yan siyasa, masu kuɗi da wasu masu riƙe da sarautar gargajiya, sai kuma wazanda suke yi wa ‘yan ta’adda leƙen asiri wato (informers).
Maganar gaskiya ita ce, idan har ana so Nijeriya ta hau kan saitin doron arziki da mutunci, to tilas sai hukumomi sun ji tsoron Allah, kuma dole sai sun daina zalunci.
Sannan ayi duk abinda za a yi wajen kawo ƙarshen ta’addanci a Nijeriya, doka da oda ta yi aiki, daga kan kansila har zuwa shugaban ƙasa duk suji tsoron Allah, su saka kishin ƙasa da al’umma a gaba ya zamo shi ne farko a zukatansu.
Wannan shi zai kawo ƙarshen cin hanci da rashawa, da satar kuɗin al’umma, da fashi da makami, da dukkan wani ta’addanci da ake yi a ƙasar nan. Idan aka yi haka Nijeriya za ta gyaru, a samar da wutar lantarki, a inganta kiwon lafiya, ilimi, tsaro, hanyoyi, ruwan sha da sauransu. Talakawa za su daina ƙyashi ga juna, zumunci da zaman lafiya zai wanzu, tattalin arzikin ƙasa zai haɓɓaka.
Amma fa duk wannan zai faru ne idan an daina cin hanci da rashawa a Nijeriya, idan an daina mulkin zalunci, idan an daina wawure kuɗin ƙasa, idan an tabbatar da doka da oda a kan kowa.
Daga NAFI’U SALISU.
Marubuci/manazarci. [email protected]. [email protected]. 08038981211-09056507471.
