Buhari da sauransu sun taya Osinbajo Murnar cika shekara 64 da haihuwa

Daga FATUHU MUSTAPHA

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari tare da sauran fitattun ‘yan Nijeriya sun taya Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo, murnar cika shekara 64 da haihuwa.

Shugaba Buhari ya bayyana Osinbajo a matsayin mutum tsayayye wanda ba ya sake da ayyukansa. Buhari ya faɗi haka cikin wata sanarwa da ta fito ta hannun mai magana da yawunsa, Garba Shehu.

A cewar Buhari, “Osinbajo mutanen mai sauƙin kai wanda ke kallon buƙatar Nijeriya a kan saura buqatu. Ɗan siyasa ne mai haƙuri kuma mai amfani da ilimi wajen aiwatar da ayyukansa.”

Daga nan, Buhari yaw a mataimakin nasa fatan alheri tare da fatan sake ganin shekaru masu yawa kuma masu albarka a gaba gami da kariyar Ubangiji.

Shi ma Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan, ya aika da saƙon taya murna ga Osinbajo ta hannun mai ba shi shawara kan sha’anin yaɗa labarai, Ola Awoniyi, inda ya addu’ar Allah ya qara wa Mataimakin Shugaban Ƙasar hikima da lafiya mai inganci domin samun damar ci gaba da tallafa wa Shugaba Buhari a gwamnatinsa mai yi wa Nijeriya hidima.

Bugu da ƙari, shi ma Shugaban Majalisar Wakila, Femi Gbajabiamila ya bi sahun ‘yan Nijeriya wajen yi wa Osinbajo fatan alheri dangane da cikansa shekara 64 da haihuwa. Tare da bayyanana shi a matsayin wanda ke yi wa ƙasarsa ta gado hidima musamman tun bayan da ya zama Mataimaki Shugaban Qasa a 2015.

Mataimakin Shugaban Majalisar Wakila, Ahmed Wase, Gwamnan jihar Legas, Bababjide Sanwo-Olu da sauransu, su ma ba a bar su baya ba wajen taya Osinbajo murnar zagayowar wannan rana.

An haifi Yemi Osinbajo ne a ran 8 ga Maris, 1957 inda ya cika shekara 64 da haihuwa a wannan Litinin, 8 ga Maris, 2021.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *