Buhari ya nuna alhininsa kan rasuwar Janar Wushishi

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya shiga cikin jerin ‘yan ƙasa da ke ci gaba da nuna alhininsu dangane da rasuwar tsohon Shugaban Rundunar Sojojin Nijeriya, Janar Mohammed Inuwa Wushishi, tare da bayyana rasuwar marigayin a matsayin babban rashi ga ƙasa baki ɗaya.

Buhari ya ce gudunmawar da marigayin ya bayar ga cigaban ƙasa a halin rayuwarsu abu ne mara misaltuwa.

Sanarwar da ta fito ta hannu mai magana da yawun Buhari, Malam Garba Shehu a jiya Lahadi, ta nuna Buhari ya ce, “Janar Wushishi ya yi aiki mai tsafta a matsyinsa na soja kuma muna alfahari da irin gudunmawar da ya bai wa ƙasa.”

Ya ƙara da cewa, “Janar Wushishi cikakken mai biyayya ne a bakin aiki da kuma sadaukarwa, kuma ya zama abin koyi ga manya da ƙanan hafsoshi.”

Daga nan Buhari ya yi amfani da wannan dama wajen miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin da Sojojin Nijeriya haɗa da Gwamnatin Jihar Neja da ma al’ummar jihar baki ɗaya.

Gwamnatin Neja ta bada sanarwar rasuwar marigayin ran Asabar da ta gabata, inda ta ce marigayin ya rasu ne a wani asibitin London bayan da ya yi rayuwa na tsawon shekaru 81.

Janar Wushishi ya riƙe muƙamin shugaban rundunar sojoji ne a jamhuriya ta biyu ƙarƙashin mulkin Shehu Shagari.

An haifi marigayin ne a ranar 1 ga Janairun 1940 a garin Wushishi cikin Ƙaramar Hukumar Wushishi a jihar Neja.