Amarya a Zamfara ta nemi saki mako guda da tarewarta saboda girman mazakutar mijinta

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Wata mata mai suna Aisha Dannupuwa da ta yi aure mako ɗaya da ya gabata a Jihar Zamfara, ta roƙi kotun shari’ar Musulunci da ta raba aurenta.

Matar da ke zaune a yankin Samaru cikin ƙaramar hukumar Gusau ta jihar ta ce, dalilin da ya sa ta buƙaci a raba auren na ta shi ne saboda girman mazakutar mijinta.

Da ta ke ba da labarin abin da ya faru, ta bayyana cewa, jima’i da mijinta a daren aurensu na farko ya yi matuƙar tada ma ta da hankali.

Aisha Dannupuwa, ta ce, “lokacin da ya zo mu yi jima’i, abin da ya faru ya kasance mai ban firgici, inda a maimakon jin daɗin jima’i, sai ya zama wani abu daban, don azzakarinsa ya yi girma da yawa, wanda a haƙiƙanin gaskiya na kan ji kamar kashe ni zai yi.”

Ta ƙara da cewa, “bayan kwana biyu, lokacin da ya ziyarce ni, mun sake yin jima’i, amma abin ya wuce gona da iri. A lokacin ne na san ba zan iya ci gaba da zaman aure da shi ba, saboda girman azzakarinsa.”

Tuni dai mijin nata, ya yarda da shawarar matar, sannan kuma ya amince da ya sake ta, kamar yadda ta nema a gaban kotun Musuluncin.